Rundunar 'Yan Sanda Ta Cafke Jami'inta Bisa Halaka Dan Kasuwa
- Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta cafke wani jami'inta bisa zargin aikata laifin halaka wani ɗan kasuwa
- Ana tuhumar jami'in ɗan sandan da laifin halaka wani ɗan kasuwa har lahira bayan ya ƙi bashi cin hanci
- Rundunar ƴan sandan ta bayar da tabbaci wajen ganin cewa ta yiwa iyalan mamacin adalci
Jihar Delta- Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta kama wani Insfetan ƴan sanda, Obi Abri, bisa zargin halaka wani ɗan kasuwa, Onyeka Ibe, a wurin duba ababen hawa kan titin Ugabolu-Illah a birnin Asaba na jihar.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Edafe Bright, ya bayyana hakan a wani dogon rubutu da yayi a shafin sa na Twitter ranar Laraba.
A rubutun na sa mai taken ‘Zargin kisan wani Onyeka Ibe' Edafe ya rubuta cewa:
"An gano insfetan ɗan sandan, an cafke shi, an taso keyar sa sannan an tsare shi."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Rundunar ƴan sanda tana bayar da tabbacin ga al'umma da iyalan mamacin zata yi adalci."
"An fara gudanar da bincike sannan za tura shi zuwa kotun domin fuskantar tuhuma."
Yadda dan kasuwan ya rasa ransa
Jaridar Punch ta samo cewa Onyeka da matarsa suna kan hanyar su ta zuwa wani waje a jihar lokacin da wasu ƴan sanda suka tsayar da motar su a wani wajen duba ababen hawa.
Bayan sun tsayar da su, ɗaya daga cikin ƴan sanda ya nemi Onyeka ya bashi N100, wacce ya kuma bashi ɗin.
Bayan ya bashi naira ɗarin, sai ɗan sandan Obri Abri ya sake zuwa masa da buƙatar ya ƙara masa wasu kuɗin amma sai ɗan kasuwar ya ƙi.
Hakan ya sanya cece-kuce ya ɓarke a tsakanin su wanda yayi munin da har ta kai Abri ya harbi Onyeka a kansa.
An Gurfanar Da 'Yan Aikin Gida Gaban Kotun Kan Zargin Satar Zinare a Kano
A wani labarin na daban kuma, an gurfanar da wasu ƴan aikin gida da ake zargi da aikata laifin halin ɓera a jihar Kano.
Ƴan aikin gidan an gurfanar da su ne a gaban kotun shari'ar musulunci kan zarfin satar zinare na miliyoyin kuɗi a gidan da suke samun na abinci.
Asali: Legit.ng