Karancin Naira: Laifin Gwamnan CBN Emefiele Ta Fi Magudin Zabe Muni, Wole Soyinka

Karancin Naira: Laifin Gwamnan CBN Emefiele Ta Fi Magudin Zabe Muni, Wole Soyinka

  • Fitaccen marubuci, Wole Soyinka ya ce laifin gwamnan babban banki kan karancin kudi ya fi na magudin zabe in a ka yi la'akari da halin da ya jefa mutane
  • Soyinka ya ce an tauye hakkin dan Adam musamman hakkin masu kananan sana'o'i saboda ba kudin siyan gyada, jarida ko guguru
  • Babban bankin kasa CBN ya ce yana iya bakin kokari don daidaita matsalar cinkoson huldar yanar gizo, tare da bayyana cewa cinkoson na faruwa ne sakamakon rufdugu da aka yi akan huldar yanar gizo

Wanda ya lashe kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya caccaki gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, akan batun sauya fasalin naira da kuma karancin rashin kudin da ya jefa kasar cikin matsi.

Soyinka a wata hira da shi a Channels TV ya ce laifin Emefiele ya sabawa yancin dan adam kuma munin laifin yafi magu-magu (magudi da yarbanci) na zabe.

Kara karanta wannan

Yadda Karancin Naira Ya Kashe Kasuwancin Miliyoyin Mutane a ‘Yan Watanni – ASBON

Soyinka da Emefiele
Wole Soyinka ya ce laifin Emefiele ta fi magudin zabe muni. Hoto: Wole Soyinka
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda ya taba cin kyautan Nobel din ya ce:

"Emefiele ya aikata laifin da ya sabawa yancin dan Adam, fiye da kowanne irin mago mago (magudi) zabe.
"Ya toshe duk wata hanya da ke tallafawa cigaban rayuwa, kananan bukatu da hakkin gama garin mutane da ke tituna."

Buhari ne ya kyale Soyinka ya jefa yan Najeriya cikin wahala - Soyinka

A ra'ayin Soyinka, Shugaba Muhammadu Buhari ne ya kyale Emefiele ya bar yan Najeriya su sha wahala.

"Kar ka dakatar da ni. Kar ka hana ni magana, hakkin tattalin arzikina. Kar ka jefa ni bakin ciki kamar Emefiele," in ji shi.
"Shi da ubangidansa, Buhari, saboda duk wata dama ta na hannunsa [Buhari] da ya bari haka ta faru. Amma shi [Emefiele] shi ne kwarararren. Shi ya bada shawarar, shi ya zartar da dokar."

Kara karanta wannan

Babbar Magana: 'Yan Sanda Sun Mamaye Babbar Sakatariyar Jam'iyya, Sun Kwace Iko Da Ita

Soyinka ya zargi gwamnan CBN da jefa kasar nan halin kunci

Da ya ke bayyana irin halin da ya shiga, dan gwagwarmayar ya ce:

"Ko a kwanaki kadan da suka gabata, da na tura takarda banki an dawo da takardar, ba su da kudin.
"Daya daga cikin ma'aikatan bankin ya kawo min wani abu daga aljihunsa ya kuma yi min bayanin halin da ake ciki, yadda suke zaman jiran a kawo kudi.
"Ba za ka iya siyan jarida ba. Ba za ka iya siyan guguru ba da gyada, wanda ke nufin ba za ka iya siyan agada ba; hakan na nufin manomi ba zai iya biyan kudin motar da za a kai kaya daga gonarsa zuwa kasuwa ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel