Kogi: Yadda Yan Bindiga Sun Sheƙe Tare da Ƙonawa Mutane Gidaje

Kogi: Yadda Yan Bindiga Sun Sheƙe Tare da Ƙonawa Mutane Gidaje

  • Jihar Kogi ta haɗu da iftila'in hari daga yan bindiga, inda wasu mahara masu yawa suka kaddamar da mummunan hari
  • Maharan sun isa yankin ɗauke da muggan makamai, tare da yin harbin kan me uwa da wabi a karamar hukumar Dekina
  • Wasu daga Maharan, sun cinnawa gidaje wuta, hakan yasa wani shugaban jam'iyyar APC da wasu mutane masu yawa suka rasa rayuwar su ta sanadiyyar harin

Kogi - Da safiyar Lahadin data gabata ne wasu mutane da ba'a san ko su waye ba, suka ƙone gidaje tare da kashe mutane a wani hari da suka kai mazaɓar Oganenigu, karamar hukumar Dekina dake jihar Kogi.

Jaridar Daily Trust ta zayyano cewar, maharan sunyi wa garin dirar mikiya ne akan abubuwa hawa masu yawan gaske, ɗauke da muggan makamai.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Buɗe Wuta, Sun Kashe Mutane Akalla 15 Ana Tsaka da Sallah a Masallaci

Wani mazaunin garin, yace masu harin sun yi harbin kan mai uwa da wabi ga duk wanda sukai ido biyu dashi, a yayin da wasu suka bazama cinnawa gidaje wuta.

Gwamnan Kogi
Kogi: Yadda Yan Bindiga Suka Sheƙa Mutane Barzahu Tare da Ƙona Musu Gidaje Hoto: Legit.ng

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana kyautata zaton James Adah wanda yake shugaban jam'iyyar APC na mazaɓar Oganenigu, James Adah, na daga cikin waɗanda suka rigamu gidan gaskiya a yayin ƙaddamar da harin.

Bugu da ƙari, mazauna yankin sun shaidawa Jaridar Daily Trust cewa, sojoji daga barikin sojiji na Oguma dake Bassa sun isa wajen ne bayan ɓata-garin sun bar wajen.

"An samu rashin tabbas a cikin al'ummar mu. mutane da yawa sun tsere zuwa Iyale, Ikpakpala, Odolu da sauran wurare domin tsira da ran su, yayin da wasu basu san inda zasu je ba, suna nan a baje kan hanyar Abejukollo-Anyigba", inji wani mazaunin garin, mai suna Richard Adejo.

Kara karanta wannan

Ana Ramandan, Yan Addinin Gargajiya Sun Kai Hari Masallaci Sun Raunata Liman Da Wasu Mutane Da Dama A Osun

Ƙoƙarin zantawa da kakakin yan sandan jihar Kogi, SP William Aya, ya samu cikas domin wayarsa ta kasance a kashe.

Kakakin hukumar kuma yaƙi biyo sakon karta-kwana da aka aika masa daga manema labarai.

A nashi ɓangaren, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, kira yayi ga mazauna yankin da su kwantar da hankali game da harin daya bayyana kira a matsayin:

"Harin rashin imani da aka ƙaddamar akan mutane masu son zaman lafiya"
"Gwamnati na zata ci gaba da fatattakar masu cin abinci da rikici daga jihar, kuma duk mai hannu a ciki zai zo hannu, ya girbi abinda ya shuka ".

Ya kuma jaddada zai saka ƙudi masu nauyi a harkar tsaro domin tabbatar da masu laifi sun girbi abinda suka shuka.

An ƙwamushe 26, tare da Sheƙa 6 Barzahu Sakamakon Harin Yan Bindiga

Jaridar Legit.ng ta ruwaito yadda wasu mahara suka kai hari a garin Naija da yayi sanadiyar rasuwar mutane 7 tare da yin awon gaba da 26.

Rahoton ya tabbatar da harin ya afku ne a ƙaramar hukumar Mashegu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel