Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 15 Ana Tsaka da Sallah Bayan Shan Ruwa a Taraba

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 15 Ana Tsaka da Sallah Bayan Shan Ruwa a Taraba

  • 'Yan bindiga sun kashe mutane 15 a kauyen Garin Baka da ke karamar hukumar Ardo-Kola a jihar Taraba
  • Wani mazaunin garin ya bayyana cewa maharan sun shigo ana tsaka da Sallah a Masallaci da daren ranar Jumu'a
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Taraba ya tabbatar da faruwar lamarin

Taraba - Wasu tsagerun 'yan bindiga kusan 60 sun kai kazamin hari ƙauyen Garin Baka da ke ƙaramar hukumar Arɗo Kola, jihar Taraba, sun kashe akalla mutane 15.

Daily Trust ta tattaro cewa 'yan bindigan sun kutsa kai cikin ƙauyen da misalin ƙarfe 7:30 na dare ranar Jumu'a, suka bude wuta ta kowane ɓangare.

Harin yan bindiga a Taraba.
Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 15 Ana Tsaka da Sallah Bayan Shan Ruwa a Taraba Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Haka nan wasu bayanai sun nuna cewa maharan sun banka wa gidaje wuta, sun tattara dabbobin jama'a da kayayyakin amfani sun yi awon gaba da su.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jiragen Rundunar Soji Sun Yi Mummunan Hatsari, Mutane da Yawa Sun Mutu

Wani mazaunin kauyen, Yakubu Garba, ya ce lokacin da 'yan ta'addan suka shiga garin, da yawan mutane suna cikin Masallaci suna sallah bayan shan ruwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce bisa tilas suka dakatar da Sallah kuma garin ya shiga matsanancin tashin hankali yayin da mutane suka fara gudun neman tsira.

Garba ya ce wasu mazauna kauyen da yawa sun ruga cikin daji domin tsira da rayuwarsu kuma biyu daga cikin iyalansa na cikin adadin waɗanda suka mutu a harin.

Ya ƙara da cewa adadin yawan mutanen da suka mutu, "Zai iya zarce 15," saboda da yawan waɗanda sun gudu zuwa cikin jeji da raunukan harbin bindiga a jikinsu.

A cewarsa, zuwa yanzun sun gano gawarwaki 10, yayin da mazauna da suka ƙunshi mata da kananan yara sun ɓata ba'a san inda suka shiga ba.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wasu 'yan kutse sun shiga jihar Arewa, sun hallaka masunta 4 da magidanci

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Yakubu Garba ya tabbatar da cewa mahukunta sun turo dakarun Soji da 'yan sanda kauyen domin dawo da zaman lafiya.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Taraba, SP Usman Abdullahi, ya tabbatar da kai harin amma ya gaza bayyana gaskiyar adadin mutanen da suka mutu.

A cewarsa, hukumar na jiran rahoto a hukumance daga Caji Ofis ɗin Sunkani.

Yan Ta'adda da Dama Sun Mutu Yayin da Suka Kaiwa Yan Sanda Hari

A wani labarin kuma 'Yan ta'adda ne suka kwashi kashinsu a hannu yayin da suka yi yunkurin kai kaiwa yan sanda hari a Abiya

A wata sanarwa, kwamishinan 'yan sandan jihar ya ce sun samu nasarar dakile harin, kuma sun kashe yan ta'addan da dama a musayar wuta.

Wasu mazauna yankin da lamarin ya faru sun ba da shaidar abinda ya faru kuma ya saɓa wa sanarwan da rundunar yan sanda ta fitar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun harbe jami'an gwamnati na NSCDC 3, a wata jiha

Asali: Legit.ng

Online view pixel