Ana Ramandan, Yan Addinin Gargajiya Sun Kai Hari Masallaci Sun Raunata Liman Da Wasu Mutane Da Dama A Osun

Ana Ramandan, Yan Addinin Gargajiya Sun Kai Hari Masallaci Sun Raunata Liman Da Wasu Mutane Da Dama A Osun

  • Wani hari da mibiya addinin gargajiya na Oro suka kai har masallaci kan mabiya addinin musulunci ya jikkata mutane
  • Harin da aka kai a garin Ille-Ife da ke Jihar Osun ya haifar da zanga zanga daga mabiya musulunci don neman a bi musu hakkinsu
  • Hukumar yan sanda da fadar Ooni na Ife sun ce ana cigaba da bincike kan lamarin tare da rokon a zauna lafiya

Osun - Mabiya addinin musulunci a Ille-Ife, Jihar Osun, ranar Juma'a, sun gudanar da zanga zanga bayan zargin kutse cikin masallaci a yankin Ilare da wasu mabiya Oro suka yi, rahoton The Punch.

Masu zanga zangar sun ce ranar Alhamis, yan gargajiyar sun shiga masallaci, inda wasu musulmi ke gudanar da sallah misalin 4:00 na yamma, suka kuma farmaki wanda suka samu a ciki.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Buɗe Wuta, Sun Kashe Mutane Akalla 15 Ana Tsaka da Sallah a Masallaci

Jihar Osun
Yan addinin gargajiya sun kai hari masallaci a Osun. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan limamin masallacin, Abdul-Lateef Adediran, wanda aka ruwaito yaji ciwo a fuska, wasu masu gudanar da ibada biyar suma ana zargin an daba musu wuka yayin harin.

Wani shaidar gani da ido, wanda ya bayyana kansa a matsayin Kareem saboda dalilan tsaro, ya ce:

"Muna masallaci don yin sallah. Wasu na gefe suna alwala lokacin da mabiya Oro suka shigo masallaci.
"Mun san za su yi zagaye da Oro kuma bamu shiga harkar su ba. Sun wuce ta wajen. Sai su ka dawo su ka shiga masallacin.
"Liman ya na kokarin tambayar me ya kawo su, amma basu bari ya yi magana ba suka fara dukan daya a cikin mu. Sun sari mutane shida. Limaminmu ya ji ciwo a fuska. Duk wanda suka ji ciwo an kai su asibiti a Ille-Ife."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: An Kam Shugaban Inyamurai Da Ya Yi Barazanar Kai Yan IPOB Lagas

Lokacin zanga zangar ranar Juma'a, masu zanga zangar sun zagaya manyan titunan garin, sun kai ziyara fadar Ooni na Ife, amma basu samu sarki ba, Sahara Reporters ta rahoto.

Sun bukaci a kama wanda ke da hannu a harin.

Daya daga cikin masu zanga zangar, Tajudeen Adesiyan, wanda ya zanta da yan jarida, ya ce sun shigar da korafi ga yan sanda, ya kara da cewa mabiyan Oro sun kawo makamancin harin a watan Nuwambar shekarar da ta gabata.

Martanin yan sandan Osun

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Osun, Yemisi Opalola, ya ce an shawo kan al'amura yayin da su ke cigaba da bincike don gano tare da hukunta duk wanda ke da hannu.

Mai magana da yawun Ooni, Moses Olafare, ya ce masarautar Ife tana kan bincika lamarin.

"Jagororin musulmi a Ife sun shiga tattaunawar zaman lafiya da ake yi. Musulmi, mabiya addinin gargajiya, da kiristoci da ke rayuwa a garin suna gudanar da taron zaman lafiya tsahon lokaci.

Kara karanta wannan

Wasu Yan Uwa Mata 6 A Gombe Sun Maka Basarake A Kotu Kan Gonar Gado

"Baba Ooni ya na kira ga duk wanda abin ya shafa zauna lafiya. Jami'an tsaro, jagororin mabiya addinin gargajiya da na musulmi su na tattauna don shawo kan lamarin," a cewar Olafare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel