Yau IGP Da Sauran Manyan Jami'an 'Yan Sanda 200 Suke Ritaya Daga Aiki

Yau IGP Da Sauran Manyan Jami'an 'Yan Sanda 200 Suke Ritaya Daga Aiki

  • Ana ta zaman jiran rashin tabbas yayin da yakamata ace shugaban rundunar ƴan sandan Najeriya yayi ritaya a yau
  • IGP Usman Baba Alkali a yau ne wa'adin shekarun sa na aiki suka cika cif-cif, inda yakamata yayi bankwana daga aiki
  • Sai dai akwai rashin tabbas kan ko shugaba Buhari zai umurce shi ya cigaba da riƙe muƙamin sa ko kuma ya aje aikin sa

Abuja- Bayan kwashe shekara 35 suna hidimtawa ƙasa, shugaban ƴan sandan Najeriya, Usman Baba Alkali da wasu manyan jami'an ƴan sanda 200, yau ne yakamata su yi ritaya daga aiki. Rahoton Thisday

Usman Baba ya cika shekara 35 yana aikin ɗan sanda a ranar 1 ga watan Maris 2023.

Usman Baba
Yau IGP Da Sauran Manyan Jami'an 'Yan Sanda Suke Ritaya Daga Aiki Hoto: Tribune
Asali: Twitter

Sai dai, a watan Janairu, ministan harkokin ƴan sanda Mohammed Dingyadi, ya bayyana cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ƙara masa wa'adin shekara biyu akan kujerar sa.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare: An Fallasa Ɗan Takarar Shugaban Kasan da Peter Obi Ya Yi Wa Aiki a Zaɓen 2023

Ministan yayi bayanin cewa shugaba Buhari yayi hakan ne domin yin biyayya ga sabuwar dokar ƴan sanda ta shekarar 2020.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dokar tayi tanadin cewa duk jami'in ɗan sandan da za a naɗa muƙamin IGP, sai ya kasance yana da sauran shekara huɗu kafin yayi ritaya.

Dingyadi ya kuma yi bayanin cewa wannan ƙara wa'adin na Usman Baba, an yi shine domin tabbatar da wannan dokar.

Sai dai, hukumar harkokin ƴan sanda ta ƙasa (PSC) ta bayyana cewa sam ba wannan hurumin ƙarin wa'adin ga jami'an ƴan sanda masu ritaya ciki kuwa harda IGP.

An samo cewa tuni har wasu manyan jami'an ƴan sanda sun fara rububin neman kujerar idan shugaba Buhari ya yanke shawarar ƙin ƙara wa'adin Usman Baba.

Idan Buhari ya bi doka, yana iya umurtar IGP ya miƙa ragamar aiki ga babban mataimakin shugaban ƴan sanda (DIG), har zuwa lokacin da za a sanar da sabon IGP.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya Sun Dira Caji Ofis na Yan Sanda, Sun Lallasa Wani Jami'in Dan Sanda

Babban DIG ɗin dai ɗan asalin jihar Katsina ne, kuma watanni tara kawai suka rage masa kafin yayi ritaya. Rahoton The Street Journal

Na Kashe Mutane Sama Da 15 A Katsina Amma Ina Neman Afuwa, Ɗan Ta'adda Mai Shekaru 28 Da Dubunsa Ta Cika

A wani labarin na daban kuma, wani ɗan ta'adda ya shiga hannun hukuma a jihar. Yace yana neman afuwa.

Ɗan ta'addan dai ya amsa cewa ya halaka sama da mutum 15 a jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel