Sojojin Najeriya Sun Tsinkayi Caji Ofis Cike Da Ƴan Sanda Tare da Gyarawa Wani ɗan Sanda Zama

Sojojin Najeriya Sun Tsinkayi Caji Ofis Cike Da Ƴan Sanda Tare da Gyarawa Wani ɗan Sanda Zama

  • Wani faifan vidiyo daya karade kafar sadarwa ta zamani ya nuna yadda ɗan sanda yake ta kai kawo cikin yanayi na kasa rashin sukuni
  • Duk da dan sandan na zagaye da ƴan uwan sa wanda suke suma a fusace. An hange su suna lallashin sa akan yayi haƙuri
  • A wani yanayi na fafatawa, anjiyo wani ɗan sanda na faɗin "ku bani tear gas ɗina, Ku bani hayaƙi mai sanya hawayena na tashe shi."

Wata balahira data tashi ta janyo kace nace a kafar majalisu da kuma kafar sadarwa ta zamani.

Lamarin ya afku ne yayin da sojojin Najeriya na ruwa suka tsinkayi wani caji ofis ɗin ƴan sanda, suka kuma gyarawa wani ɗan sanda zama kamar yadda wani faifan bidiyo ya nuna a kafar sadarwa ta Twitter.

Lamarin dai ya faru ne a ranar juma'a, can cikin jihar Delta dake kudu maso kudun tarayyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Hukumar NDLEA Ta Soma Daukar Aiki: Ta Lissafa Sharruda 7 Ga Masu Niyyar Nema

Police
Sojojin Najeriya Sun Tsinkayi Caji Ofis Cike Da Ƴan Sanda Tare da Gyarawa Wani ɗan Sanda Zama Hoto: Premiumtimes.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sa-toka-sa-katsin ta afku ne a Caji ofis ɗin Enerhen, can kusa da Warri, kamar yadda wanda ya saki faifan bidiyon ya wallafa tare da rubutawa.

Bidiyon mai daƙiƙa 30, ya nuna yadda ɗan sandan ya kasa zaune, ya kasa tsaye.

Inda daga gefe kuma, ƴan uwansa ƴan sanda dake cikin caji ofis ɗin na Enerhen ke faman lallashin sa, duk da cewa suma ran su a ɓace yake.

Kai da ganin sa kasan maza sunji jiki, domin fuskar sa akwai jini, yayin da kayan jikin sa suka cukurkuɗe harda yagewa.

"Kingsley, natsu. Kada ka ɗauki doka a hannun ka,"

wata murya take faɗi a bayan fagen vidiyon.

"Ni ku ƙyale Ni,"

Inji ɗan sandan da yasha mazga.

Tuni ɗan sandan daya sha masga ya cire rigar tasa ya kuma yi fitar ɓurgu gamida tunkarar babbar ƙofar harabar caji ofis ɗin domin bin bayan sojojin da ake zargi sun saɓa masa kamanni.

Kara karanta wannan

Karar Ƙwana: Yadda Wasu Miyagun Ɓarayi Suka Halaka Wani Yaro a Gonar Mahaifin Sa

Bidiyon ya nuna yadda ya fita daga ƙofar harabar wajen da sauri, inda yaci burki a wajen wasu masu sanye da kayan sojoji ɗan taƙi kaɗan daga ƙofar harabar wajen.

Daga bisani kuma, na'urar ɗaukan vidiyon an sunkuyar da kanta ƙasa inda aka daina ganin komai sai dai murya.

Muryar taci gaba da cewa:

"Taku ta ƙare muku! Taku ta ƙare muku!

Inji muryar dake bayan fage take faɗi lokacin da take Allah wadai da abinda suka aikata.

Muryar taci gaba da faɗin:

"Akan me zaku daki ɗan sanda a cikin ɗa caji ofis."

inji muryar.

Daga nan ne sai kamarar ta ƙara matsawa kusa zuwa wajen ɗaya daga cikin sojan daya wayance da kiran waya, sannan ta ƙara zuwa wajen wani sojan da wani ɗan sandan ya riga da afka mawa.

Sai wata murya tace:

"Kada ka barsu su tafi fa, Kada kuyi wannan kuskuren.

Kara karanta wannan

Yadda Hankalin Wata Mata Ya Tashi Gamida Dugunzuma Saboda Kama Diyarta da Wani a Otel.

Inji muryar. Sannan ta kara da cewa:

Ku bani tear gas ɗina, Ku bani hayaƙi mai sanya hawaye na na tashe shi."

Bidiyon sai ya ƙare bagatatan bayan wani sahu ya tsinkaye na'urar, wanda da alama na gudu ne. Wanda watakila gudun ɗauko hayaƙi mai sanya hawayen aka tafi yi.

Majiya bata samu damar gano musabbabin al'amarin ba yayin haɗa wannan rahoton.

Kuma duk wani ƙokari da Jaridar Premium Times tayi na gano hakan ta hannun kakakin yan sandan Delta, Bright Edafe abin yaci tura.

Inda yace:

"Lamarin na cikin gida ne, kuma muna yin abinda ya dace".

Mahukuntan sojojin ruwan Najeriya har yau basu saki wani bayani akan faruwar lamarin ba.

Ana Fama Da Karancin Naira, NSCDC Ta Kama Wasu Gungun Mutane 'Masu Buga Jabun Sabbin Naira Da Daloli

NSDCDC ta samu kama wasu gungun mutane da suka ƙware wajen haɗa dalolin Amurka na jabu suna rabawa mutane suna amsar kuɗin gaske na Naira.

Kara karanta wannan

Muna Jiran Hukuncin Kotun ƙoli Akan Lamarin Shekarau Inji NNPP

Olusola Odumosu shine kakakin hukumar, yace an samu wannan gagarumar nasarar ne a garin Jos.

Odumosu yace tawagogi ne masu yawa amma ɗaya cikin tawagar, sun haɗa da maza hudu, an kama su ne ɗauke da dallar Amurka ta bogi 64,800 da N475,000.

Sannan yace an samu nasarar ƙwato jabun kudi har naira miliyan 1.5 daga hannun tawagar ta biyu da ta kunshi maza biyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel