“Bana Yi”: Matashiya Ta Fallasa Magidanci Da Ke Nemanta, Ta Sako Matarsa a Zancen

“Bana Yi”: Matashiya Ta Fallasa Magidanci Da Ke Nemanta, Ta Sako Matarsa a Zancen

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta caccaki wani magidanci mai suna Linus, wanda ta zarga da nemanta da lalata
  • Matashiyar ta ce bata so kwancewa magidancin zani a kasuwa ba amma sai ya fara zafin 'ya'yanta saboda ta ki amincewa da bukatarsa
  • Da take ambatar matar mutumin a Facebook, ta yi alkawarin sakin hotunan wautarsa don duniya ta gani

Wata mata yar Najeriya mai suna Judyjams Chinenyenwa Emukai ta fallasa wani magidangi mai suna Linus kan damunta da yake da batun soyayya duk da cewar yana da aure.

Chinenyenwa ta ambaci sunan matar Linus, Buttered Peace Nwunye Linus, a Facebook yayin da ta bukaci matar da ta janye mijinta daga yi mata sako ta DM.

Sako da Matashi
“Bana Yi”: Budurwa Ta Fallasa Magidanci Da Ke Nemanta, Ta Sako Matarsa a Zancen Hoto: Maazi Ogbonnaya Okoro II, Muhammad Musbahu Goni
Asali: Getty Images

Chinenyenwa ta ce da haka kawai ne za ta yi watsi da sakonnin mutumin amma dole ta sauya tunani saboda yana zaginta da yaranta bayan ta ki amsa tayinsa.

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Manyan Arewa Sun Fada Wa Shugaba Buhari Abinda Zai Faru Idan Ya Ki Bin Umarnin Kotun Koli

Ta kara da cewar Linus ya yi alkawarin sakin matarsa idan ta yarda ta yi soyayya da shi. Matar ta bayyana shi a matsayin wawa akuya sannan ta sha alwashin sakin hotunan wawancinsa a soshiyal midiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An dauki hoton wallafa tata wanda ta goge a yanzu kuma ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

Mawallafin harshe kuma marubuci Maazi Ogbonna Okoro ya rubutun nata wanda ta goge a Facebook, inda ya bayyana shi a matsayin abun kunya.

Jama'a sun yi martani

Osarhieme Owen Eze ya ce:

“Mutumin ne ya nuna rashin tarbiya.
“Matar ce ta zo ta sha kashi....
“Inda addu’a ta zata dosa a wannan safiya ta Lahadi.”

Shomie Thickana ta ce:

“Me yasa za ta ambaci sunan matar da bata san hawa ba bata san sauka ba? Menene laifin da ta aikata?

Kara karanta wannan

Toh fa: An sanyawa masallaci sunan gwamna Kirista, kungiyar Musulmai ta yi martani

“Me yasa bata aikawa matar sakon sirri ba sannan ta fallasa mutumin a bainar jama’a ba?
“Menene laifin matar???
“Toh ta fallasa dukkanin sakonnin akwatinta tunda wasan kwaikwayo take son yi, da ace mai kudi ne yanzu ci zata yi ta goge baki ya kai kan Linus kina ambatar matarsa.”

A wani labarin, jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan cin karo da bidiyon wani buki da mahalarta taron suka dungi hararar amarya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel