"Ku yafe min dan Allah": Inji Direban Motan da Yayi Kicibis da Jirgin Ƙasa a Lagos Mutum 6 Suka Mutu

"Ku yafe min dan Allah": Inji Direban Motan da Yayi Kicibis da Jirgin Ƙasa a Lagos Mutum 6 Suka Mutu

  • Mahaya motar bas ɗin da suka tsira suna zargin Direban da yin kemadagas da gargaɗin karya tsallaka titin Jirgin ƙasan
  • Sunce direban ya sanya abin jin sauti a kunnen sa, ya nanawa mota wuta, ya tunkari titin jirgin duk da gargadin yalo-fifa
  • Gamuwar motar da jirgin aka ji wani sauti tamkar aradu zata faɗo, direban ko ƙwarzane baiyi ba, amma mutane 6 sun mutu

A ranar Alhamis ɗin data gabata ne dai aka haɗu da wani iftila'in taho mu gama da jirgin ƙasa da motar bas a Lagos.

Hatsarin da yayi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane shida, tare da jikkata gommai.

Direban motar da haɗarin ya rutsa dashi mai suna Oluwaseun Osinbajo, ya roƙi gafara da neman yafiya daga waɗanda abin ya rutsa dasu da kuma wadanda ya shafa.

Kara karanta wannan

Babban Jigo Kuma Tsohon Gwamna Ya Bar Inuwar Atiku Zuwa APC? Gaskiya Ta Bayyana

Jirgin kasa
Ku yafe min dan Allah Inji Direban Daya Ja Mota ta Haɗu da Jirgin Ƙasa a Lagos 6 Suka Sheka Barzahu Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tunda da fari dai, mahaya motar bas ɗin sun zargi matuƙin motar dake da shekaru 44 a duniya akan kada ya tsallaka titin amma yaƙi.

Sun ce yana sanye da abubuwan jin sauti a kunnuwan sane, yayin da yake tukin kuma yayi ƙemadagas da umarnin da masu bada hannun titin jirgin ƙasan suka yayi masa akan ya tsaya.

Direban mai suna Osinbajo, yace motar ce birkin ta ya ƙi ci shi yasa ya kasa tsayawa.

Direban da yake aiki da ma'aikatar sufuri ta jihar Lagos, tuni aka maida shi sashen binciken manya laifuka na SCID bayan tsira da yayi daga hatsarin batare da yaji ko ƙwarzane ba daga hatsarin.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, ta jiyo Direban yana faɗawa ƴan uwan sa cewar:

"Ba laifi na bane. Tayaya zan ƙi sauraren gargaɗin masu kula da hanya?

Kara karanta wannan

Ramadan: Malamin Addini Yayi Kira Ga CBN Da Ya Saki Takardun Kuɗi Isassu

"Ina rokon kowa da kowa, da a taimaka a yafe min, dan Allah."

Sojojin Najeriya Sun Tsinkayi Caji Ofis Cike Da Ƴan Sanda Tare da Gyarawa Wani ɗan Sanda Zama

Wannan diramar mai ban takaici da dariya ta faru ne a wani gari dake can jihar Delta, Kudu Maso Kudancin Najeriya.

An hangi vidiyon Lamarin mai daƙiƙa 30, ya nuna yadda ɗan sandan ya kasa zaune, ya kasa tsaye. Yan uwan sa suna lallashin sa, wanda alamu ke nuna ya dibi kashin sa a hannun sa.

Yayin da wani ɗan sanda yace abashi hayaƙi mai sanya hawaye domin ya tasar wa sojojin da suke ƙoƙarin kiran waya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel