Yadda Hankalin Wata Mata Ya Tashi Gamida Dugunzuma Saboda Kama Diyarta da Wani a Otel.

Yadda Hankalin Wata Mata Ya Tashi Gamida Dugunzuma Saboda Kama Diyarta da Wani a Otel.

  • Wata mata da ta kama diyar ta da gardi a hotel ta zabga ihu saboda mamaki
  • To amma ta kece da dariya sanda ɗiyar ta waigo taga yadaa mahaifiyar ta shiga ruɗu
  • Mutanen dake dandalin sadarwa na zamani, sun tofa albarkacin bakinsu akan vidiyon mai ban dariya

A lokuta da dama iyaye sukan samu ɗiyar su a wani yanayi da basu zata ba.

Hakan na faruwane ga jinsin maza ko mata. Yanayin daka iya zama na farin ciki ko akasin haka.

Wani lokacin yanayin ka iya zama duka biyun, wato farin ciki da bakin ciki a hade

tiktok
Yadda Hankalin Wata Mata Ya Tashi Gamida Dugunzuma Saboda Kama Diyarta da Wani a Otel. Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda ya faru a wani faifan vidiyo da yake tashe a kafar sadarwa ta zamani yayin da wata mata ta kama ɗiyar ta a Otel.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Aure Mahaifin Tsohon Saurayinta Bayan Rabuwa da Shi

A Bidiyon an nuna yadda yarinyar take kanannaɗe da hannun ta a jikin wani mutum , akan hanyar su ta fitowa daga Otel din.

Koda Mahaifiyar yarinyar ta ganta a wannan yanayi, sai ta carke tare da zabga wani ihu cike da ƙaraji na firgici ganin yanayin da suke da kuma sanin daga inda suka fito.

Koda yarinyar taji ƙarajin mahaifiyar tane, sai tayi maza ta waigo inda ita ma abin ya ɗaure mata kai ganin mahaifiyar ta wajen.

A wani salo na "Kanku ake ji" mutumin da suke da yarinyar sai yaci gaba da yin murmushi abinsa, yana ɗaukar su hoto mai motsi a waya.

Bidiyon mai ban al'ajabi da dariya an saka ma taken:....

"Yar auta ta, ina ta kewar rashin ganin ki a ciki shekarar nan gabaki daya, amma sai naganki a ranar ƙarshe da shekarar nan a haka".

Bidiyon ya janyo hankula al'ummar kafar sadarwa ta intanet sun tofa albarkacin bakinsu:

Kara karanta wannan

Ali Ya Ga Ali: Bidiyon Yadda Budurwa Ta Yi Kicibis Da Iyayenta a “Go Slow” Tana Gaggawa Ta Koma Gida Don Ta Yi Dare a Waje

Tia tace:

"Abin ban dariya, dariyar ki abar ban dariya ce"

Tiona:

"Haka ake son mutum, ina matuƙar yi miki murna yar uwa".

User-Lango:

"Yadda kika yi fuska, kika basar yayi matuƙar burgeni".

Mogomotsi:

"Yarinya ta gama yarda zata bada kai bori yahau, amma umma tace wane mutum".

Corky Mak yace:

"Ta shiɗe gabaki daya rayuwar ta"

Social butterfly yace:

"Hahaha,Yadda tayi zillo, ta kalli mahaifiyar ne abu mafi burgewa."

Yeahno yace:

"Awww ko kun fahimci shima ya taya ta sambaɗo samfurin mamaki? Ku kalli murmushin dake fuskar sa.

Gina tace:

"saura kaɗan su fahimci juna su"

Sojoji Sun Kai Samame Sansanin Yan bindiga, Sun Ceto Kwamishina a Kuros Riba

A wani labarin kuwa, Sojojin Najeriya sun yi nasarar kubutar da kwamishinar harkokin mata ta jihar Kuros Ribas daga hannun masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

“Muna Alfahari Da Ke”: Bidiyon Karamar Yarinya Tana Tuka Tuwo a Kan Murhu Kamar Babba Ya Girgiza Intanet

A wata sanarwa da rundunar ta 13 da ke Kalaba ta fitar, ta ce bayan samun bayanai, Dakaru suka kai samame mafakarbata garin.

A halin yanzu kwamishinar na karɓan magani a hannun sojoji kafin daga bisani su sallameta ta koma cikin iyalai.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel