Masu magana da yaren Hausa sun kai miliyan 120 a Najeriya

Masu magana da yaren Hausa sun kai miliyan 120 a Najeriya

Yawan masu magana da harshen Hausa a Najeriya ya kai kimanin miliyan 120, cewar wani sanarwa.

Wannan na cikin wata sanarwa da aka bayar a ranar Alhamis a karshen wani taron kwana daya da sashin harsunan Afrika da al’adu, na jami’ar Ahmed Bello (ABU) dake Zaria jihar Kaduna suka shirya.

Sanarwan wanda ke dauke da sanya hannun Dakta Balarabe Danladi aka kuma bayyana wa hukumar News Agency of Nigeria (NAN), yace yawan mutane dake amfani da harshen yare shi ke sawa a mayar da shi harshen kasa baki daya.

Wannan ya kasance ne saboda ana yaren a fadin duniya an kuma rarraba masu yaren zuwa wandanda yake yarensu da kuma masu aron yaren.

A Najeriya, Hausawan asali sun dara miliyan 70 yayinda masu aron harshen wadanda ke amfani da harshen Hausa a matsayin yare na biyu sun kasance tsakanin miliyan 40 da 50 bisa ga kimantawa, ya kara da cewa.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta bada Umarnin sakin shugaban yan Shi'a El-Zakzaky

Binciken ya kuma nuna cewa ta gano cewa sama da daya da kwatan yawan yan Najeriya, suna jin yaren Hausa, kuma sanadiyar yaduwar yaren, a ciki da wajen Najeriya ya sa harshen Hausa ya zama harshen tarayyar al’umma a Najeriya.

Wannan matsayi ya sa gwamnati ta inganta harshen Hausa zuwa yaren da akeyi a fadin Najeriya cikin sauki.

An ce ana amfani da harshen Hausa a masallatai, cocina, a gurin kasuwanci da kuma gurin sauran ayyukan siyasa da na zaman takewa.

Sanarwan yace harshen Hausa bai tsaya a gida kawai ba a’a har a kasashen waje an san da harshen Hausa wannan na daga cikin dalilan da yasa ake shirin mayar da harshen na kasa baki daya.

An ce an san da harshen Hausa a kasashen waje a fanni daban-daban kamar irin su Microsoft, jami’oin kasashen waje, kafofin watsa labaran kasa-da-kasa, shafin zumuntana Facebook da sauran ayyukan kasa-da-kasa, tallafi ga yaren asali, musamman Hausa, zai taimaka gurin kawo ci gaba da inganci a kasa. (NAN)

Asali: Legit.ng

Online view pixel