CBN ta Dakatar da Bankunan Yanar Gizo daga Budewa Sababbin Kwastomomi Akawun

CBN ta Dakatar da Bankunan Yanar Gizo daga Budewa Sababbin Kwastomomi Akawun

  • Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankunan yanar gizo da su dakata da budewa sababbin kwastomomi asusu daga yanzu
  • Bankunan da abin ya shafa sun hada da Opay, Palmpay, Kuda da Moniepoint da sauran irin wadannan bankunan masu hada-hada ta yanar gizo
  • Ana zargin wasu na amfani da asusun da ke bankunan wajen daukar nauyin ta'addanci da halasta kudin haram, da sauran ayyukan laifi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Babban bankin Najeriya (CBN) ya dakatar da kamfanonin bankuna ta yanar gizo da su dakata da yi wa sabbin kwastomomi rajista.

Bankunan yanar gizon da lamarin ya shafa sun hada da Opay, Kuda Bank, Monie point da Palmpay.

Kara karanta wannan

Lamari ya lalace; Gwamantin jihar Kano ta saka dokar ta baci a kan harkar ilimi

An dakatar da budewa sabbin kwastomomi asuss a bankunan yanar gizo
Ana zargin wasu na haramtacciyar hada-hada ta asusun Hoto:Central Bank of Nigeria Asali:Twitter
Asali: Facebook

Punch News ta ruwaito cewa wata majiya a CBN din ta ce ba a fitar da sanarwa a hukumance kan hakan ba, amma an sanar da bankunan su dakata da budewa sabbin kwastomomin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin bankuna da haramtacciyar hada-hada

Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin wasu na amfani da asusu a bankunan tafi da gidanka na gudanar da haramtacciyar hada-hada.

Mai Shari'a Emeka Nwite na babban kotun tarayya Abuja ya ba hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) damar rufe asusu 1,146 da ake zargi da haramtacciyar mu'amala.

Ana kuma zargin ana amfani da asusun wajen daukar nauyin ta'addanci da halasta kudin haram, kamar yadda Channels Televsion ta wallafa.

Mai Shari'a Emeka Nwite ya bayar da umarnin ci gaba da rufe bankunan har sai an kammala bincike.

Kara karanta wannan

IMF: Falana ya fadi wadanda suka 'ingiza' Gwamnatin Najeriya ta kara kudin wuta

Za a bude sabon bankin yanar gizo

Mun ruwaito a baya cewa shahararren dan kasuwa, Alhaji Sa'adina Dantata ya samar da sabon bankin yanar gizo mai suna Kayi bank a babba birnin tarayya Abuja.

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Bosun Tijjani ne ya kaddamar da bankin da ake sa ran zai yi gogayya da irinsu Opay da Kuda da Moniepoint.

A jawabin da Alhaji Sa'adina Dantata ya yi, ya ce ana sa ran samar da sabon bankin zai magance matsalolin fasaha da na tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel