Amfanin Zogale goma sha takwas (18) Ga Jikin Dan-Adam

Amfanin Zogale goma sha takwas (18) Ga Jikin Dan-Adam

Legit.ng ta kawo muku amfanin Zogale domin kiwon lafiyan al'umma ba tare da zuwa asibiti ba. Gabanin zuwan turawa, malam Bahaushe ya shahara da amfani da ganye da kayan itace wajen magani.

1- Ana dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi domin maganin Olsa (ulcer).

2- Ana shafa danyen ganyen zogale akan goshi domin maganin ciwon kai.

3- Ga wanda ya yanke ko ya sare ko wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen ganyen zogale inshaAllah jinin zai tsaya.

4- Ga mai fama da kuraje a jiki, ya hada garin zogale da man zaitun ya shafa.

5- Ana sanya garin zogale akan wani rauni ko gembo domin saurin warkewa.

6- Sanya garin zogale a cikin abinci yana maganin hawan-jini da kuma karama mutum kuzari.

KU KARANTA: Zabe: Yan siyasa na kwasar dalibai a matsayin yan bangan siyasa – Sarki Sanusi

7- Ana dafa ganyen zogale tare da sa kanwa 'yar kadan domin maganin ciwon shawara.

8- Ga mai fama da ciwon ido zai diga ruwan danyen zogale, haka ma mai fama da ciwon kunne.

9- Macen da ke shayarwa ta dafa furen zogale da zuma dan karin nono.

10-Wanda ke fama da yawan fitsari wato cutar Diyabetis ya rinka shan furen zogale da citta kamar shayi.

11-Idan aka tafasa furen zogale da albasa aka sha kamar shayi yana maganin sanyi.

12-Haka ma cin danyen zogale yana maganin tsutsar ciki ga yara.

13-Ana daka ganyen zogale da 'ya'yan baure a sha da nono ko kunu yana maganin ciwon hanta.

14-Ga mai fama da sanyin kashi ko wani kumburi zai soya 'ya'yan zogale a daka su sannan a hada da man kwakwa (man-ja) sai a shafa.

15-A daka zangarniyar zogale da 'ya'yan da ke ciki tare da karanfani, citta, masoro da kuma kimba domin karin karfin da namiji da sa masa kuzari, haka kuma yana karawa mata nishadi.

16-A daka saiwar zogale da 'ya'yan kankana a sha da nono yana maganin tsakuwar ciki (Apendis).

17-Haka kuma idan mutum yana fama da ciwon Kanjamau zogale kan radadinshi ta hanyar shan ruwan dafaffen zogale.

18-Haka kuma mai fama da Typhoid da malaria da kuma ciwon basir ko shawara, zai iya yawaita shan ruwan dafaffen zogalen domin samun sauki.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel