"Jami'an DSS Na Yi Mana Bita-da-kulli": Yan Jam'iyyar NNPP Sun Koka a Kano

"Jami'an DSS Na Yi Mana Bita-da-kulli": Yan Jam'iyyar NNPP Sun Koka a Kano

  • Jam'iyyar NNPP ta koka kan yadda jami'an DSS suka dira ofishohin kamfensu dake jihar Kano
  • NNPP ta zargi DSS da bita-da-kulli tare da kitsa sharri ta hanyar zuba makamai ofishohinsu
  • Hukumar DSS ta ce babu ruwanta da siyasa kuma ayyukanta kawai ta shiga gudanarwa ofishin na NNPP

Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Kano ta tuhumci jami'an hukumar tsaron farin kaya, DSS, da cin zarafin mambobinta ta hanyar kai musu hare-hare ofishoshin kamfe a jihar, rahoton DailyTrust.

Wannan tuhuma na zuwa ne ana saura yan kwanaki zaben shugaban kasa da yan majalisar dokokin tarayya,

Tutar NNPP
Tutun Yan Jam'iyyar NNPP a Kano Hoto: NNPP
Asali: UGC

Haka kwanakin baya jam'iyyar tayi zargin cewa hukumar yan sanda na hada kai da gwamnatin jihar wajen cin mutunci da damke mambobinta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC Jahili ne: Cewar Gwamnatin Kogi Bayan Kotu Ta Kwace Wasu Kadarorin Gwamnanta

Bayan hakan Sifeto Janar na hukumar yan sanda, Usman Baba, ya sauya kwamishanan yan sanda jihar Kano, inda ya turashi jihar Plateau sannan ya turo kwamishanoni biyu sabbi zuwa Kano don gudanar da zabe.

Shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ra ranar Laraba ya bayyanawa manema labarai cewa jami'an DSS sun kai hari ofishohin diraktocin kungiyoyin magoya bayansu da kuma ofishin diraktan hada kan matasa na jam'iyyar.

Yace:

"Mun ka'du matuka bisa yadda jami'an DSS ke fito da makamai daga cikin motocinsu suna zubawa cikin ofishohin dirkatocinmu. A gaban ma'aikatan ofishohin akayi haka, kuma an na'di hakan a bidiyo. Muna da hotuna da bidiyoyin wannan kaidi."
"Muna kira da Dirakta Janar na DSS ta tsawatar da na Kano."

Amma hukumar DSS tayi martanin gaggawa inda tace ayyukanta na halas ta tafi gudanarwa kuma ta gano makamai a ofishoshin wasu yan siyasa.

Yayinda aka tuntubi kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, ya bayyana cewa bindigogi, takkuba da wukake jami'anta suka bankado a hannun wasu yan siyasa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: An kai muhimman kayan aikin zabe shugaban kasa jihar Gombe, INEC ta magantu

DailyTrust tace Afunanya ya turo mata wasu hotuna na makaman da aka bankado daga ofishohin.

Yace:

"Da izinin doka aka gudanar da harin. Ba gaskiya bane DSS a Kano na yiwa wata jam'iyyar siyasa bita-da-kulli."

Gwamnatin Kogi Tayi Alla-Wadai Da EFCC Bayan Kwace Wasu Kadarorin Gwamna Yahaya Da Kotu Tayi

A wani labarin kuwa, gwamnatin jihar Kogi ta caccaki shugaban hukumar EFCC, AbdulRashed Bawa, bisa yiwa gwamnanta bita da kulli.

Kwamishanan labaran jihar ya ce Bawa jahili ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel