Hukumar INEC, Hukumomin Tsaro, Jam’iyyun Siyasa Sun Kai Ziyara A Jihar Gombe

Hukumar INEC, Hukumomin Tsaro, Jam’iyyun Siyasa Sun Kai Ziyara A Jihar Gombe

  • Yayin da ya sauya kwanaki uku kacal a yi zaben 2023, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta dauko kayan aikin zabe daga CBN
  • A jihar Gombe, an nunawa masu ruwa da tsaki a zaben bana kayayyakin da za a yi amfani dasu a ranar Asabar 25 ga watan Faburairu
  • Ana ci gaba da kai kayayyakin zabe jihohi don tunkarar zaben bana, lamarin da ke ci gaba da daukar hankali a Najeriya

Jihar Gombe - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a ranar Laraba 22 Faburairu, 2023 ta duba kuri’un da za a yi amfani dasu a zaben ranar Asabar mai zuwa a jihar Gombe.

Wadannan kayayyaki masu muhimmanci dai an ajiye su a wani ofishin Babban Bankin Najeriya da ke hanyar Kano a jihar ta Gombe, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An Yi Kus-Kus Tsakanin Shugaban INEC Da Shugaba Buhari Game Da Zaben Ranar Asabar

Jam’iyyun siyasa, masu sanya ido kan zabe da sauran hukumomin tsaro na daga cikin wadanda suka duba kayayyakin na kananan hukumomi 11 na jihar.

An raba kayan zabe a jihar Gombe
Kadan daga cikin kayayyakin da aka raba na zabe a jihar Gombe | Hoto: Punch Newspaper
Asali: Facebook

An shirya komai, zabe na nan daram a jihar Gombe, inji kwamishinan INEC

Da yake tabbatar da komai na muhimman kayayyakin na nan kasa, kwamishinan zabe, Ibrahim Umar ya ce hukumar a shirye take don yin zabe na gaskiya na shugaban kasa da majalisun tarayya a jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, nuna kayayyakin wani yunkuri ne na bayyana gaskiyar shirin INEC ga yin zaben, inda ya kara da cewa, hukumar na tsammanin samun hadin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki a harkar zabe.

Jaridar Punch ta yada hotunan kayayyakin da aka rarraba na kananan hukumomin jihar Gombe.

Jihar Gombe na daya daga cikin jihohin shiyyar Arewa maso Gabas da jam'iyyar APC ke mulki, siyasar jihar na daukar hankalin yankunan kasar nan da yawa.

Kara karanta wannan

Da Dumi: Shirin Zabe Na Ta Kankama, Hukumar Zabe Ta INEC Ta Fara Rarraba Muhimman Kayan Aikin Zabe

INEC Ta Fara Rabon Muhimman Kayan Aikin Zabe

A wani labarin kuma, kun ji yadda hukumar zabe ta fara raba kayan aikin zabe ga ofishoshinta na kanan hukumomi daban-daban na kasar gabanin zaben bana.

Rahoto ya bayyana cewa, tuni an rarraba kayayyakin aikin zaben a jihar Ribas, jihar PDP da ke Kudancin Najeriya kuma daya daga cikin wadanda za su kada kuri’a a zaben bana.

An ruwaito cewa, an ga jami’an tsaro kama daga ‘yan sanda har zuwa jami’an NSCDC a wurin duba kayayyaki, kuma an tabbatar da tsaro da amincin yin zabe a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel