Tashin Hankali: Bam Ya Hallaka Mutane 28 a Jihar Nasarawa

Tashin Hankali: Bam Ya Hallaka Mutane 28 a Jihar Nasarawa

  • Wasu Fulani makiyaya sun gamu da ajalinsu a jihar Nasarawa sakamakon tashim Bam da ya rutsa da da
  • Kawo yau Alhamis, kwamishanan yan sanda ya ce mutum ashirin da takwas ne suka mutu
  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya roki Fulani kada suce zasu dau fansa kan al'umma

Nasarawa - Akalla Fulani Makiyaya 27 suka rasa rayukansu yayinda Bam ya tashi da daren Talata a karamar hukumar Doma ta jihar Nasarawa.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Ramhan Nansel, ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Laraba a Lafia, rahoton Punch.

Nansel ya bayyana cewa Bam din ya tashi ne a garin Rukubi, iyakan jihar Nasarawa da Benue.

Ya ce hukumar na hada kai da sauran hukumomin tsaro wajen binciken abinda ya haddasa tashin Bam.

Yace:

Kara karanta wannan

Katsina: Buhari ya Isa Jihar Katsina Daga Dawowarsa Senegal, Gwamna Masari da Ayarinsa Sun Masa Tarbar Karamci

"Da ban takaici irin wannan abun ya fari. makiyaya ashirin da bakwai suka mutu bayan tashin Bam a karamar hukumar Doma."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Hukumar yan sanda da abokanta na aiki tukuru domin fahimtar abinda ya faru tare da bibiyan wadanda suke da hannu ciki."
Nasarawa
Tashin Hankali: Bam Ya Hallaka Mutane 27 a Jihar Nasarawa
Asali: UGC

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya lashi takobin cewa zai dauki mataki kan wadanda suka aikata wannan abin.

Gwamnan ya yi kira ga Fulani makiyaya a fadin jihar su kwantar da hankulansu.

Jawabin kwamishanan yan sandan jihar

Kwamishanan yan sandan jihar, Miayaki Muhammad, a jawabin da ya yiwa ChannelsTV a Lafia, birnin jihar Nasarawa.

A cewarsa:

"Sun tafi amsa Shanunsu da jami'an tsaron Benue suka kwace ne. Daga nan sai suka ji karar tashin Bam din da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Dakatar Da Kamfe Saboda Babban Rashi Da Ta Yi A Imo

"A iya ilimina, kawo jiya (Laraba), mutum 27 aka bizne. Bayanin dake iso mana yanzu shine akwai wanda aka kai asibiti a Lafia kuma yanzu ya mutu."
"Labarin da muke da shi yanzu kenan, bamu da wani."

Al'umma Sun Shiga Tashin Hankali Yayin Da Bam Ya Kase Mutane Da Dama a Babban Jihar Arewa

A wani labarin kuwa, mutane da dama sun rasu sakamakon tashin Bam a garin Galkogo, Karamar hukumar Shiroro, Jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an mayakan saman Najeriya, NAF, ne suka yi ruwan wuta daga jiragen yaki yayinda suke neman yan bindiga masu garkuwa da mutane a Neja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel