Matashi Ya Kera Motar Wasan Tsere, Ya Tuka Ta a Birnin Edo, Mutane Sun Sha Mamaki a Bidiyo

Matashi Ya Kera Motar Wasan Tsere, Ya Tuka Ta a Birnin Edo, Mutane Sun Sha Mamaki a Bidiyo

  • Wani hazikin matashi dan Najeriya ya haddasa cunkoso a wata hanya a jihar Edo bayan ya tuko motar da ya kera da hannunsa
  • Wannan bajinta da matashin ya yi ya sa mutane sun kewaye shi yayin da suke jinjina kokarinta
  • Motar ya burge masu amfani da soshiyal midiya sannan sun koka kan yadda mutane irinsa basa samun tallafi daga wadanda ke rike da madafun iko

Wani matashi dan Najeriya ya yadu a soshiyal midiya bayan an gano shi yana tuka motar wasan tsere da ya kera da hannunsa a jihar Edo.

Wata matashiya da ke kan hanyar lokacin da matashin ya wuce ta dauki bidiyonsa sannan ta wallafa a TikTok, cewa abun ya bata mamaki.

Motar wasan tsere
Matashi Ya Kera Motar Wasanni, Ya Tuka Ta a Birnin Edo, Mutane Sun Sha Mamaki a Bidiyo Hoto: TikTok/@faithgold214
Asali: UGC

Ba ita kadai wannan abu da yaron ya yi ya burge ba. Kamar yadda aka gani a bidiyon, masu wucewa sun taru a wajen hazikin yaron yayin da ya tsaya.

Kara karanta wannan

Bidiyon Zabgegiyar Damisa Tana Takun Isa Cikin Jama'a Da ke Shakatawa ya Janyo Cece-kuce

Wasu sun taba jikin motar don jin yadda yake. An radawa motar suna da King Don. Da Aka Tambayeta game da inda abun ya faru, budurwar ta sanar da Legit.ng cewa ta ga motar ne a Auchi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai kuma, har yanzu bata sanar Legitng game da yadda za ta hadu da yaron ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Steph.any ta ce:

"Mu yan Najeriya Allah ya yi mana baiwa da hazaka koda dai...kawai bamu da wasu kayayyaki ne."

rashford857 ta ce:

"Na rantse ba mu da shugabanni a kasar nan, ba sa taba taimako na gaji da kasar nan dubi baiwa."

Quency ta ce:

"Yesu ya kamata Obi Cubana ya kalli wannan a ina yaron nan yake? Irin wadannan yaran ya kamata ya dunga taimakawa."

Kara karanta wannan

Kyakyawar Baturiya Ta Tafi Da Saurayinta Dan Najeriya Kasarsu Don Ya Gana Da Danginta, Bidiyon Ya Kayatar

Kan Du ya ce:

"Tsantar baiwa amma abun da ke bani mamaki sosai shine a wannan nahiya ta Afrika ko haramun ne."

gucciqueen304:

"Wow abun ya yi kyau Allah ya yiwa Najeriya baiwa."

Sagasty Bae:

"Duk da haka shugabanninmu ba za su gani ba....suna da madafun iko ba hikima sannan muna da hikima ba madafun iko."

Matashi ya kera motar kara harda saka mata injin, ya tayar da abarsa

A wani labarin, mun ji cewa jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan cin karo da wata motar kara da matashi ya kera tare da saka mata injin, ya tayar da ita inda ya zagaya gari a cikinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel