Kyawawan Hotuna Sun Bayyana Yayin da Yar Najeriya Ta Dankarawa Iyayenta Gida Na Gani Na Fada

Kyawawan Hotuna Sun Bayyana Yayin da Yar Najeriya Ta Dankarawa Iyayenta Gida Na Gani Na Fada

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta mayar da iyayenta irin gidan da take mafarki yayin da hotunan dankareren gidan ya yadu a soshiyal midiya
  • Matashiyar mai suna Sugar BSN ta ce ta dade tanba burin yiwa iyayenta wani abu na musamman a rayuwa
  • A cewarta, sun yi mata komai a rayuwa sannan sun yi aiki tukuru tare da sadaukar mata da abubuwa a rayuwa don haka ta gwangwaje su da wannan alkhairin

Wata matashiya yar Najeriya ta cika da farin ciki bayan ta mayar da iyayenta wani hadadden sabon gida.

Matashiyar mai suna Sugar BSN ta saki hotunan dankararen gidan a Twitter.

Iyali, gida da budurwa
Kyawawan Hotuna Sun Bayyana Yayin da Yar Najeriya Ta Dankarawa Iyayenta Gida Na Gani Na Fada Hoto: Twitter/@MylifeasSugar.
Asali: Twitter

Sugar ta ce iyayenta sun karar da rayuwarsu wajen aiki da sadaukarwa iyalin don haka ta gwangwaje su da wannan gagarumin kyauta.

Yar Najeriya ta yi wa iyayenta kyautan katon gida

Kara karanta wannan

An Samu Babbar Matsala: Wasu Jiragen Sama Sun Yi Karo a Sararin Samaniya, Rayuka Sun Salwanta

A cewarta, ya kasance babban burinta yi wa iyayenta abun kaunarta wani gagarumin abu na musamman a rayuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yanzu mafarkinta ya zama gaskiya kuma sabon gidan ya burge masu amfani da soshiyal midiya da dama.

A hotunan da ta wallafa a ranar 31 ga watan Disamba, mahaifiya da mahaifin Sugar sun gaza boye farin cikinsu lokacin da aka yi masu jagoranci zuwa hadadden gidan.

Sun durkusa cikin farin ciki da hannayensu a sama don nuna godiya ga Allah a kan wannan gagarumin kyauta.

Da take wallafa hotunan, Sugar ta rubuta:

"Bayan dogon lokaci na aiki da sadaukarwa, a karshe na mayar da iyayena gidan da suke mafarkin samu. Da nake girma, ban taba mantawa da gwagwarmayar da muka fuskanta kuma a kodayaushe ina son yi ma iyayena abu na musamman. Na gode Allah kuma wannan shine lokaci mafi soyuwa a rayuwana."

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Sharbi Kuka a Bidiyo, Ta Sha Alwashin Lallasa Mahaifinta Kan Kawo Abokiyar Sharholiyarsa Gida

Jama'a sun yi martani

@biodun_alao ya ce:

"Wannan gagarumi ne kuma abun burgewa matuka. Kin yi kokari sosai. Allah ya albarkace ki."

@spicyprincess01 ta ce:

"Wannan hadadden gida ne. Allah na rokeka ka albarkace ni sannan ka bani arzikin da nake bukata don yiwa iyayena irin haka. Ina tayaki da iyayen murna."

@Yemijoel3 ta yi martani:

"Na shiga sahun miliyoyin mutane da ke alfahari da ke wajen tayaki murna. Kin yi kokari!"

Budurwa ta sharbi kuka bayan mahaifinta ya halarci taron iyali da budurwarsa

A wani labarin kuma, wata matashiya ta yi fushi matuka da mahaifinta kan ya halarci taron iyali da abokiyar sharholiyarsa.

Budurwar wacce ta sharbi kuka ta yi barazanar lallasa mahaifin nata a kan cin mutuncin da ya yi masu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel