Budurwa Ta Sharbi Kuka Wiwi, Ta Yi Barazanar Dukan Mahaifinta Kan Zuwa Taron Iyali Da Budurwarsa

Budurwa Ta Sharbi Kuka Wiwi, Ta Yi Barazanar Dukan Mahaifinta Kan Zuwa Taron Iyali Da Budurwarsa

  • An gano wata matashiyar budurwa a bidiyo tana barazanar dambe da mahaifinta kan cin mutuncinsu
  • Matashiyar sanye da jan tufafi ta sha kuka wiwi a gaban kowa a wajen wani taro na iyali yayin da ta ga laifin mahaifinta kan zuwa taron da budurwarsa
  • Kamar yadda aka gani a bidiyon, mutane sun yi kokarin tausar fusatacciyar matashiyar sannan sun janye ta daga tunkarar dattijon mutumin

Bidiyon wata matashiya tana barazanar dukan mahaifinta a wani taron iyali ya haddasa cece-kuce.

Budurwa da mahaifinta
Budurwa Ta Sharbi Kuka Wiwi, Ta Yi Barazanar Dukan Mahaifinta Kan Zuwa Taron Iyali Da Budurwarsa Hoto: Mariana Mariana/ TikTok.
Asali: UGC

A cewar mutumin wanda ya wallafa bidiyon a TikTok, an dauki faifan ne a yankin Kisumu.

Budurwa ta kusa lallasa mahaifinta

Bidiyon ya nuno matashiyar tana sharban kuka wiwi kuma har ta tunkari mahaifin nata kan halartan taron da abokiyar sharholiyarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

"Nan Zan Kwana" Bidiyon Yadda Wani Mutumi Ya Gigita Diyarsa Yayin da Ya Shiga Dakin Tsohuwar Matarsa Ya Tube Kaya

Kyakkyawar matashiyar budurwar ta yi fushi sosai da dattijon mahaifin nata kan zuwa gida da ya yi da wata mace.

Ba don dandazon jama'ar da suka tare ta ba da matashiyar wacce ke sanye da jan kaya ta farmaki mahaifinsu.

An jiyo wasu yan uwansu suna gargadinta kan idan ta isa ta daura hannunta a kan dattijon yayin da sauran ke kare mahaifin nata.

Mariana Mariana ce ta fara wallafa bidiyon a TikTok amma sai wani dan kasar ya sake yada shi a Twitter.

Bidiyon ya haifar da zazzafan martani a soshiyal midiya yayin da wasu da dama ke ganin laifin matashiyar.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@NishaMillicent ta ce:

"Amma me yasa maza suka zabi cin mutuncin iyalansu??? Me zai sa shi halartan irin wannan taron da budurwa?"

@bryan_mobysah:

"Mahaifin bai da wani dalili na yi mata nayamo, shi ba mijinta bane."

@c_cheii ta ce:

Kara karanta wannan

Shin suna zubewa? 'Yan Najeriya suna ta wanke sabbin Naira don gwada ingancinsu

"Za ta samu abun da bata yi tunani ba."

Matashi ya kama kofar gidansu ya rufe, ya hana manemin auren kanwarsa da mutanensa shiga

A wani labarin kuma, wani matashi shirya wata yar dirama yayin da ya hana saurayin da ke neman auren kanwarsa shiga cikin gidansu.

Mutumin ya kama kofa ya rufe sannan ya shimfida tabarma ya yi kwanciyarsa yayin da mutanen suke dungi rokonsa ya bude masu amma ya yi biris da su har sai da suka jefa masa kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel