Gobara ta Lamushe Rayukan Yara 2 Dake Garkame a Cikin Daki

Gobara ta Lamushe Rayukan Yara 2 Dake Garkame a Cikin Daki

  • Yara biyu sun kone kurmus sanadiyyar wata mummunar gobara da ta lashe gidansu a titin Udo Imuk na karamar hukumar Eket dake Akwa Ibom
  • An gano yadda lamarin ya auku misalin karfe 7:00 na daren Juma'a bayan mahaifiyar yaran ta kullesu a dake, inda ta shiga makwabta karbo wasu kayayyaki
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce ana bincikar musabbabin lamarin don gudun sake maimaita kansa

Akwa Ibom - Yara biyu sun kone kurmus bayan gobara ta kama gidansu a titin Udo Imuk na karamar hukumar Eket dake Akwa Ibom.

Taswirar Akwai Ibom
Gobara ta Lamushe Rayukan Yara 2 Dake Garkame a Cikin Daki. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Lamarin ya auku ne misalin karfe 7:00 na daren Juma'a.

An gano yadda iyayen yaran, 'yar shekara shida da 'yar shekara uku, suka kullesu a dakI bayan sun shiga amso kayayyaki a makwabta.

Kara karanta wannan

Ashe babu dadi: Kasurgumin dan bindiga ya firgita, an rusa gidansa, an kashe yaransa 16

Odiko Macdon, kakakin 'yan sandan jihar, ya bayyana yadda mahaifiyar 'ya'yan ta rufe yaran a dakI yayin barin gidan, hakan ya hana yaran fita.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewersa, rundunar bata gano abun da ya haddasa gobarar ba amma ana bincikar lamarin don gudun sake aukuwar hakan a gaba.

"Tabbas lamarin ya auku, abun takaici ne kwarai. Abun damuwa shine yadda mahaifiyar ta bar yaranta a gidan gami da garkame kofa, sai dai bamu san ya aka yi gobarar ta fara ci ba, abun takaici , yaran basu samu damar tsira ba har wutar ta konesu kurmus a cikin dakin.”

- Kamar yadda ya shaidawa The Cable.

"Kwamishinan 'yan sanda ya mika sakon ta'aziyya sannan rundunar na cigaba da bincike don sanin musabbabin lamarin tare da ganin an gujewa aukuwar hakan a gaba.
"Tabbas, lamarin ba shi da dadi amma muna binciken sanin musabbabin lamarin cikin gaggawa."

Kara karanta wannan

2023: Gaskiya Ta Fito, Gwamnan APC Ya Magantu Kan Rahoton Yana Yi Wa PDP Aiki

Gobara ta lashe rayukan matar aure da yaranta biyu

A wani labari na daban, wata mummunar gobara a jihar Jigawa ta tashi a wata bukka wacce matar aure da yaranta biyu ke kwance suna bacci a ciki.

Lamarin ya faru a kauye Tsangarwa dake karamar hukumar Gwaram ta jihar inda ake kyautata tsammanin rushi da suka shiga dashi dakin ne ya kama da wuta har ya halaka su suna bacci.

Ya auku da misalin karfe 11 na daren Juma'a ne a cikin tsakiyar watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel