'Yan Najeriya Sun Zo da Sabon Salo, Suna Ta Wanke Sabbin Naira Don Gwada Ingancinsu

'Yan Najeriya Sun Zo da Sabon Salo, Suna Ta Wanke Sabbin Naira Don Gwada Ingancinsu

  • ‘Yan Najeriya sun tsiri wani sabon salon kalubale a kafar sada zumunta don gwada ingancin sabbin Naira da aka buga
  • Wannan na zuwa ne bayan da wani bidiyo ya yadu na yadda sabbin kudin ke zuba yayin da aka tsoma su a ruwa
  • Mutane da yawa sun yi martani ta hanyar yada bidiyon yadda nasu kudin ya kasance; yana zubewa ko a’a

Najeriya - Biyo bayan wani bidiyon da wata mata Chinazo a kafar Twitter ta yada, inda tace kudin Najeriya sun wanke tas bayan jikewa a ruwa, ‘yan kasar da dama sun yi sabbin bidiyo sun yada a intanet.

A bidiyon da ta yada, ta ce ‘yar uwarta ta wanke gudan N500 a aljihi cikin rashin sani, wannan yasa sabon kudin ya sauya zuwa farar takarda.

Wannan lamari dai ya dauki dumi a kafar Twitter, domin kuwa mutane da yawa sun shiga mamakin yadda kudi zan kasance haka.

Kara karanta wannan

Babu Nakasasshe Sai Rage: Bidiyon Mai Nakasa Yana Kasuwanci A 'Yar Kekensa

'Yan Najeriya na wasan wanke sabbin Naira a Najeriya
'Yan Najeriya Sun Zo da Sabon Salo, Suna Ta Wanke Sabbin Naira Don Gwada Ingancinsu | Hoto: @cbn
Asali: Getty Images

A bangare guda, ‘yan kasar da dama na tambayar inganci da gaskiyar abin da matar ta yada a Twitter.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

‘Yan Najeriya na gwada ingancin sabbin Naira

Ikrarin da Chinazo ya kawo wani sabon salo a kafar sanda zumunta, mutane suka fara jikawa tare da wanke sabbin kudin ganin ko da gaske suna zuba.

Sai dai, Dr Joe Aba, wata daraktar kasa a jami’ar DAI. DAIMaastricht ya yi tsokaci tare da wani gwaji a martani ga bidiyin Chinazo.

A cewar @DrJoeAbah, tabbas zubewar sabbin kudin Naira ba gaskiya bane, sai dai idan akwai wani lauje a cikin nadi.

A cewarsa:

“Na goga sabuwar N500 da ruwa da kuma auduga. A’a, launin bai wanke ba. Watakila matsalar a jikin gudan sabuwar N1,000 ne, wanda ni ban gwada ba. Sabuwar N500 dai a wuri na bata wata matsala. Zan gwada a injin wanki sannan na ba ku rahoto daga baya.”

Kara karanta wannan

Ya Kashe Kudi Sosai a Kai: Dan Najeriya Ya Tuka Motar G-Wagon Da Ya Kera Da Kansa a Bidiyo

Another video from @__bellefille also denied the claim that the new naira notes fade colour.

Har ila yau, @__bellefille ta karyata labarin cewa da gaske sabbin kudin Najeriya na zubewa idan suka jike.

Ta yada sabon bidiyo tare da cewa:

"Ga mutanen da ke cewa wai sabbin kudade na zubewa, meye-meye-meye."

A tun farko, Chinazo ta ce 'yar uwarta ce ta wanke N500 cikin kuskure, hakan ya maida sabon kudin zuwa farar takarda tas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel