Kasuwar Crypto Ta Shiga Tasku a 2022, Bitcoin Ya Karye da 60% a Cikin Watanni 12

Kasuwar Crypto Ta Shiga Tasku a 2022, Bitcoin Ya Karye da 60% a Cikin Watanni 12

  • ‘Yan crypto sun sha wahala a shekarar 2022 da ta gabata, domin kuwa sun ga bacin rana da karayar farashin kaya a shekarar
  • Bayanai sun nuna cewa, sama da kaso 60% ne na darajar Bitcoin ya wanke tare da asarar $2.1tr a cikin shekarar
  • Wannan kuwa, ana kyautata zaton ya faru ne sakamakon alamomin tambayoyi da suka dinga tasowa daga duniyar crypto

Kasuwar Bitcoin ta sha fama a 2022 tare da ganin rugujewar farashin kaya da kuma karyewar kamfanin hada-hadarsa na FTX, wanda a yanzu ya karye kalat dakudaden jama’a.

Rahoton CNBC ya bayana cewa, akalla $2.1trn(N940.96trn) aka rasa a kasuwar crypto baki daya a duniya.

Hada-hadar crypto dai sananniyar aba ce da ba ta da tabbas kan hawa da saukar farashi, wannan yasa ake samun riba mai yawa ko asara mai tsanani.

Kara karanta wannan

Yunkurin tsige Buhari da Tirka-Tirka 10 da Aka Yi a Majalisar Tarayya a Shekarar 2022

Yadda kudaden intanet suka karye a 2022
Kasuwar Crypto Ta Shiga Tasku a 2022, Bitcoin Ya Karye da 60% a Cikin Watanni 12 | Hoto: coinmarketcap
Asali: Facebook

Saboda haka, masana harkar kasuwanci da kudade suka ba da shawarin nesantar zuba makudan kudade a ciki tukuna, kasancewar faduwar ka iya ninka ribar da za a girba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, ba kowa ne ya hango karywar kudaden crypto ba, musamman Bitcoin a bara kasancewarsa kudin intanet da aka fi sani.

Bayanai daga Coinmarketcap ya nuna cewa, farashin Bitcoin ya fara ne daga $47,680.93($47.6m), amma ta kare a $16,625.69($16.6m) a ranar 31 ga watan Disamban bara.

Jerin kudaden crypto da suka sha fama, suka karye a 2022

A kasa mun tattaro muku jerin fitattun kudaden intanet da suka samu sauyi a 2022, ga su kamar haka:

  1. Terra: -100%
  2. Solana: -93%
  3. AMP: -93%
  4. Cardano: -80%
  5. Ether: -67%
  6. Bitcoin: -63%
  7. Dogecoin: -55%

Me ake tsammanta a bana; 2023?

Karyewar kamfanin crypto na FTX mai darajar $32bn ya girgiza ‘yan crypto a duniya, kuma hakan na ci gaba da bayyana tasiri a kasuwar.

Ana tsammanin masu ‘yan crypto za su ci gaba da yin kaffa-kaffa da zuba jari a watannin uku na farkon 2023 ko ma fiye da haka har sai an samu wasu hanyoyi da ka’idojin kare hannayen jarin crypto a kasuwannin duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel