Ku Nemi Satifiket din Gwajin Kwaya Daga Manema Auren Yaranku Mata, Marwa
- Shugaban hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA, Buba Marwa, ya bukaci masu 'ya'ya mata da su nemi satifiket din gwajin kwaya daga masu son 'ya'yansu
- Marwa ya sanar da hakan ne yayin kira ga iyaye da su hada kai da hukumar wurin yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi tun daga cikin gidajensu
- Marwa ya garzaya gain Yola dake jihar Adamawa inda aka bashi lambar yabo kan aikin da yake ta yi a kasar nan wurin yakar ta'ammali da kwayoyi
Yola, Adamawa - Hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA, Janar Buba Marwa mai ritaya, yayi kira ga iyaye da su zama sahun gaba wurin yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi inda zasu fara da 'ya'yansu.
Ya jaddada cewa, akwai bukatar iyaye su fara neman satifiket din gwajin kwaya daga manema auren 'ya'yansu, Channelstv ta rahoto.
Marwa ya bayyana hakan ne a Yola, babban birnin jihar Adamawa bayan ya karba lambar yabo kan aikin da yake yi.
Channels TV ta rahoto cewa, yace akwai abubuwan da suka faru inda yara ke shan miyagun kwayoyi har su halak iyayensu. Don haka yayi kira ga masu tarbiya da su hada kai wurin yaki da miyagun kwayoyi wadanda suke bada gudumawa wurin ta'addanci a Najeriya ballantana Arewa maso Gabas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NDLEA ta Cafke Mai Juna Biyu Dauke da Miyagun Kwayoyi
A wani labari na daban, hukumar yaki da ta'ammali miyagun kwayoyi, NDLEA, ta kama wata mata mai juna biyu mai shekaru 25 dauke da kwayoyin methamphetamine a Auchi dake jihar Edo.
Femi Babafemi, kakakin NDLEA, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a Abuja ranar Lahadi.
Yanzu Yanzu: NBA Ta Bukaci a Biya Iyalan Lauya Da Aka Kashe Diyyar N5b, Ta Ba Da Kwakkwaran Dalili 1
Babafemi yace wacce ake zargin mai suna Haruna Favour, an kama ta ne a ranar Juma'a, an kama ta dauke da nau'ikan wiwi da miyagun magungunan ruwa masu dauke da ke codeine.
A cewarsa, yunkurin da wasu manyan dillalan kwayoyi suka yi na fitar da methamphetamine mai nauyin na 7.805kg zuwa Amurka da Australia, ya tarwatse yayin da jami'an NDLEA suka bankado hakan a Legas.
Babafemi ya sanar da cewa, an boye miyagun kwayoyin a gefen kayan sawa, gumakan katako, printer, hannuwan jakunkunan tafiya da garri.
Asali: Legit.ng