An Yi Girman Banza: Bidiyon Yadda Wani Saurayi Ya Sharbi Kuka Saboda Rabuwa da Budurwa

An Yi Girman Banza: Bidiyon Yadda Wani Saurayi Ya Sharbi Kuka Saboda Rabuwa da Budurwa

  • Wani matashin saurayi ya sharbi kuka kamar karamin yaro bayan wacce yake kauna ta yi barazanar kawo karshen alakarsu
  • A wani Bidiyo da aka wallafa a soshiyal midiya, idanun saurayin sun kaɗa sun yi ja sakamakon tsawon lokacin da ya dauka yana rusa kuka
  • Sai dai daga baya masoyiyar ta taya shi, Inda aka ga hawaye ya fara zuba a kumatunta domin ta rarrashi sahibinta

Mutane sun yi martani kan wani bidiyo da aka wallafa a Soshiyal Midida wanda ke ɗauke da labarin wasu masoya biyu da suka shaku da juna.

Bisa wani dalilin da ita kaɗai ta sani, wata matashiyar budurwa ta yi wa Saurayinta barazanar datse alakar soyayyar da suka jima sna ginawa.

Soyyaya ruwan zuma.
An Yi Girman Banza: Bidiyon Yadda Wani Saurayi Ya Sharbi Kuka Saboda Rabuwa da Budurwa Hoto: @precioushassan855
Asali: UGC

Sakamakon takaicin abinda kunnuwansa suka ji yo masa daga wacce yake kauna, Saurayin ya barke da rusa kuka na dagaske bai daina ba har idanunsa suka kaɗa suka yi jajir.

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Budurwa Ta Fada Tarkon Son Wani Boka, Ta Saki Zazzafan Bidiyonsu a Kogi

Budurwar wacce take ganin abinda ke faruwa, nan take ta fara kokarin lallashinsa sannan kuma ta janye kalaman da ta yi da farko na rabuwa da shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ganin masoyin na ta ya ki hakura ya ci gaba da kukansa kai kace yaro ne karami, ya ki jin lallashin da take masa, nan take itama budurwar ta kama zubda hawaye.

Bidiyon wannan abu da ya faru da tsuntsayen soyayyar biyu wanda aka wallafa a dandalin TikTok ya ja hankalin mutane da dama.

Kalli bidiyon a nan

Martanin jama'a kan lamarin

Nonny Love ta ce:

"Lallai wannan wasan na sabbin shiga fagen soyayya ne, nan ba da jimawa ba zaku raba hanya ku dai ci gaba da irin wannan wasan."

Christian Eco ya ce:

"Kai jama'a mun rasa ɗan uwanmu."

Kanneth Martin ya ce:

Kara karanta wannan

Budurwa Mai Tallan Tuwo a Najeriya Ta tsallake, Ta Tare Da Mijinta a Turai, Sun Bar Jama'a Baki Bude

"Ɗan Mama kenan su akwai taushin zuciya kuma irin waɗan nan mutane ba su iya shiga soyayya ba, mai gaba ɗaya suke yi."

Bidiyon Yadda Kare Ya Hau Sama, Ya Janyo Kusan N900k Ya Yagalgala

A wani labarin kuma Wata mata ta shiga yanayi yayin da karenta ya jawo kudi sama da N800,000 ya yagalgala su lokacin bata nan

A wani bidiyo da ta wallafa tana kuka, matar ta faɗi yadda karen nata ya haura inda kudin suke kana ya cinye kusan dalq $2000 (watauN893,260 a kuɗin Najeriya).

Lamarin dai ya haddasa cece-kuce tsakanin masu amfanu da kafafen sada zumunta, wasu sun nemi ta rungumi kaddara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel