Ana Wahala: Yadda Wani Gurgu Ya Mayar Da Kekensa Ya Zama Shagon Siyar Da Kaya, Bidiyon Ya Yauka Hankali

Ana Wahala: Yadda Wani Gurgu Ya Mayar Da Kekensa Ya Zama Shagon Siyar Da Kaya, Bidiyon Ya Yauka Hankali

  • Wani gurgu wanda ya mayar da keken guragunsa ya zama shagon siyar da kaya ya taba zukatan jama'a da dama
  • An gano mutumin a wani bidiyo da ya yadu a TikTok wanda Vincent Chika ya wallafa, ya kuma ce ya ga mutumin ne a yankin Mushin
  • Awanni 24 bayan wallafa bidiyon a ranar 27 ga watan Disamba, har yanzu yana tashe a kan TikTok inda ya samu 'likes' fiye da 9k

Wani mutumi ya wallafa bidiyon wani gurgu da ke fafutukar neman na kansa harma ya mayar da keken guragunsa ya zama wani dan karamin shagon siyar da kaya.

Dan gajeren bidiyon da aka wallafa a ranar 27 ga watan Disamba ya nuno mutumin yana tuka kekensa a titi dauke da yan kayan amfani na yau da kullun.

Shagon gurgu
Ana Wahala: Yadda Wani Gurgu Ya Mayar Da Kekensa Ya Zama Shagon Siyar Da Kaya, Bidiyon Ya Yauka Hankali Hoto: TikTok/@untitledrichway.
Asali: UGC

Vincent Chika ne ya wallafa bidiyon mai taba zuciya, ya kuma ce ya ga mutumin ne a wajajen Mushin da ke jihar Lagas.

Kara karanta wannan

Duniya ta daina min dadi: Attajiri Dantata ya fada, ya bayyana abin da ya sauya masa a rayuwa

Awanni 24 bayan ya wallafa bidiyon, mutane da dama a TikTok sun nemi sanin ta yadda za su iya taimakawa bawan Allah.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Chika ya yiwa bidiyon take da:

"Gaskiya na ji masa sosai. Ina rokon Allah yasa abubuwa su inganta sannan su yi sauki a gare shi."

Wasu sun bayyana cewa sun taba ganinsa a wannan yankin da Chika ya ambata. Yanzu haka bidiyon na da martani 212.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@kharisabigail3 ta ce:

"Kuma a haka wasu na da kafafuwa biyu da hannu biyu amma ba za su tashi neman na kai ba. Wannan rayuwar."

@kunta070777 ya yi martani:

"Dan Allah ka amsa bukata ta dan uwa koda zan zo ganinsa a Mushin zan aika maka da sako a duk lokacin da zan zo."

@user361999709723 ya ce:

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Ta Kwashe Tsakanin Soja da Wata Budurwa Bayan Ta Zage Ta Gudu, Ya Kamo Ta

"Lokacin da mahaifina ya gan shi ya siya abu a wajensa, yana da kwazon nema sosai."

@user294754189881 ya yi martani:

"Amma da ka siya abu daga wajensa."

@Daniel Ugwu461 ya ce:

"Na ga wannan gayen kamar sau biyu a Mushin."

@Bashman ya yi martani:

"A duniyar nan abun da kake bukatar yi shine neman na kai. Ina rokon Allah yasa fafutukar nan nasa ya zama alkhairi wata rana."

@anonymous_crypto ya ce:

"Mutane na wahala. Allah ka taimakemu."

@Nikki ta ce:

"Allah ya albarkaci nemansa."

Na hakura da haihuwa, Magidanci mai mata 12 da yara 102

A wani labarin, wani dattijo mai suna Musa Hasahya mai shekaru 67 wanda ke da matan aure 12 da yara 102 ya ce yanzu yana matukar fama da rayuwa don ciyar da iyalinsa.

Musa mai jikoki 568 ya ce a yanzu sun yanke shawarar amfani da kwayoyin hana daukar ciki don dakatar da iyalinsa daga ci gaba da yaduwa.

Kara karanta wannan

Ka latsa ni: Kyakkyawar budurwa ta tari wani dan Najeriya, ta nemi su fara soyayya

Asali: Legit.ng

Online view pixel