Hukumar Yan Sanda Ta Saki Jami'anta 2 Cikin Wadanda Aka Kama Kan Kisan Lauya A Legas

Hukumar Yan Sanda Ta Saki Jami'anta 2 Cikin Wadanda Aka Kama Kan Kisan Lauya A Legas

  • Kwana uku da kisan da wani jami'in dan sanda ya yiwa wata mata a Legas, an saki abokansa biyu da aka kama tare da shi
  • Hukumar yan sandan ta ce basu da hannu cikin kisan kawai an kama su ne saboda sun shaida abinda ya faru
  • Bolanle Raheem lauya ce kuma tana dauke da juna biyu na yan biyu lokacin da sandan ya bindigeta

Legas - Hukumar yan sandan jihar Legas ta bayyana cewa za'a sake jami'an yan sanda biyu da aka kama kan kisan Bolanle Raheem a jihar Legas ranar Talata.

Jami'an yan sandan na tare da ASP Dambri Vandi lokacin da ya bindige lauya mai dauke da juna biyu ranar Kirismeti.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai, NAN, ranar Talata cewa yan sandan basu da hannu cikin kisan.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Bayyana Abu 1 Da Yan Kaduna Ba Za Su Taba Manta El-Rufai a Kansa Ba

Bolanle
Hukumar Yan Sanda Ta Saki Jami'anta 2 Cikin Wadanda Aka Kama Kan Kisan Lauya A Legas
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce an damkesu ne kawai don ji ta bakinsu da kuma gudanar da bincike, rahoton TheCable.

Yace:

"Yan sanda biyu dake tare da ASP da ya kashe lauya za'a sake su ranar Talata (Jiya) bayan gabatar da jawabin ganin ido ga hukuma."
"An damkesu ke saboda sun ga abinda ya faru. Basu suka kashe matar ba."
"Sun bada labarin abinda ya faru kuma Kwamishana ya bada umurnin sakesu yayinda ake cigaba da gudanar da bincike."

Hundeyin ya ce kwamishanan yan sandan jihar, Abiodun Alabi, ya canza DPO na ofishin yan sandan Ajiwe biyo bayan kisan wani Gafaru Buraimoh ranar 7 ga Disamba.

IGP na yan sanda Alkali Baba Ya Fusata da Kisan Lauyar Legas, Yayi Umarnin Bincike da Gurfanar da ‘Dan Sandan

Sifeta janar na ‘yan sandan IGP Usman Baba Alkali, Najeriya ya yi Alla-wadai bisa kisan Bolanle Raheem da wani ASP na yan sanda ya bindige ranar Kirismeti.

Kara karanta wannan

Dan Sanda Ya Harbe Wata Lauya a Hanyarta Ta Dawowa Daga Coci a Ranar Kirsimeti

A cewarsa, za'a gudanar da bincike kuma a hukunta jami'in dan sanda.

Mahaifiyar Bolanle Raheem ta bayyana cewa sai da ta kwashe shekara da shekaru tana tallan Lemu a jihar Legas kawai don diyarta ta samu daman yin karatu ta zama lauya.

Amma sai yanzu da lokacin jin dadinta ya zo jami'in dan sanda ya kasheta kan titi ba gair aba dalili.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: