IGP Alkali Baba Yayi Umarnin Gaggauta Bincike da Gurfanar da ‘Dan Sandan da ya Halaka Lauya

IGP Alkali Baba Yayi Umarnin Gaggauta Bincike da Gurfanar da ‘Dan Sandan da ya Halaka Lauya

  • Sifate janar na 'yan sandan Najeriya, IGP Alkali Usman Baba, ya yi Allah wadai da kisan lauya Bolanle Raheem da wani 'dan sanda yayi
  • Alkali Usman Baba yayi umarnin gaggauta bincike tare da gurfanar da jami'in 'dan sanda da yayi aika-aikar
  • Ya sanar da jama'a cewa, babu shakka za a tsaya tsayin daka wurin tabbatar da cewa an yi mata adalci tare da kwato mata hakkinta

Legas - Usman Baba Alkali, Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya ya kushe kisan Bolanle Raheem, wata lauya da jami’in ‘dan sanda dake aiki da caji ofis din Ajiwe dake Ajah ta jihar Legas ya halaka, jaridar Punch ta rahoto.

Lauya Bolanle
IGP Alkali Baba Yayi Umarnin Gaggauta Bincike da Gurfanar da ‘Dan Sandan da ya Halaka Lauya. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Jaridar TheCable ta rahoto cewa, Baba ya bayar da umarnin gaggauta bincike tare da gurfanar da jami’in ‘dan sandan dake da hannu a kisan.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Nadin Mukami, Ya Zabi Budurwa a Matsayin Mai Bada Shawara Kan SDGs

An yi harbi ne yayin da marigayiyar tare da iyalanta suke dawowa daga coci ranar bikin Kirsimeti a ranar Lahadi.

Lamarin ya janyo cece-kuce mai tarin yawa inda aka dinga caccakar 'yan sanda a soshiyal midiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A yayin martani a wata takarda da kakakin rundunar Muyiwa Adejobi yasa hannu, IGP ya kwatanta lamarin da abu mara dadi da takaici.

Sifeta janar din 'yan sandan Najeriya ya jajantawa iyalai, abokai da abokain aikin marigayiyar.

Baba yace rundunar 'yan sanda ba za ta lamunci irin wannan lamarin da bai dace ba.

"Sifeta janar ya kwatanta lamarin matsayin abun takaici, ya umarnin bincike na gaggawa tare da gurfanar da 'yan sandan dake da hannu kan mugun abun, wanda baya nuna hallayar da dabi'un 'yan sandan Najeriya."

- Takardar tace.

"Har ila yau, Sifeta janar na 'yan sandan yana jaje ga iyalai, abokai da abokan aikin mamaciyar yayin da yake fatan rahama gareta.

Kara karanta wannan

Da Dumi-ɗumi: Hadimin Gwamnan Jam'iyyar APC Ya Mutu a Hatsarin Mota

“Ya kara da tabbatar da jama'a cewa a za a yi adalci a lamarin yayin da ya ja kunnen jami'an da su kasance kwararru da kuma mayar da hankali kan al'umma yayin sauke nauyin dake kansu tare da aiki da doka, saboda rundunar ba za ta lamunci irin wannan abubuwan ba ko rashin kwarewa."

Legas: 'Dan sanda ya halaka lauya

A wani labari na daban, wani jami'in 'dan sanda ya bindige wata lauya a jihar Legas.

An gano cewa, lauyar mai suna Bolanle Raheem tana dawowa daga coci ne da iyalanta yayin da ibtila'in ya ritsa da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel