Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 2 Sun Yi Awon Gaba da Wasu 10 Yayin da Suka Farmaki Al’umman Kebbi

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 2 Sun Yi Awon Gaba da Wasu 10 Yayin da Suka Farmaki Al’umman Kebbi

  • Yan bindiga sun kai kazamin hari kan al'umman garuruwan Gaye da Shangel a karamar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi
  • Mahara sun kashe mutum biyu sannan suka yi awon gaba da wasu 10 a harin na ranar Asabar
  • Tuni mutanen da ke garuruwa masu makwabtaka suka fara hada yanasu-yanasu suna ficewa saboda tsoro

Kebbi - Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun kashe mutane biyu sannan sun yi garkuwa da wasu 10 a farmakin da suka kai garuruwan Gaye da Shangel a karamar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi a ranar Asabar.

Mazauna kauyen sun ce yan bindigar sun yi awon gaba da mutum 10 a garuruwan kafin suka koma mabuyarsu da ke cikin jeji, Daily Trust ta rahoto.

Yan bindiga
Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 2 Sun Yi Awon Gaba da Wasu 10 Yayin da Suka Farmaki Al’umman Kebbi Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

Daya daga cikinsu ya ce:

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Kwana 1 da kashe tarin mutane, 'yan bindiga sun sake kai mummunan hari a Arewa

"Biyar daga cikin mutanen da suka yi awon gaba da su yan gidan wani mamba mai wakiltan Wasagu a majalisar dokokin jiha ne."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce yan bindigar sun zo da yawansu don farmakar garuruwan Gaye da Shangel a ranar Asabar.

"Sun yi mana zuwan bazata. Ba mu taba tsammanin za su zo ba, da mun dakile hare-haren. Wannan ba shine karo na farko da suke farmakar garuruwa a wannan yankin ba. A kodayaushe muna cikin shirin ko ta kwana kan hare-harensu."

Ya ce harin ya jefa mutanen da ke makwabtaka cikin yanayi na tashin hankali da fargaba, rahoton Daily Post.

Ya kara da cewar:

"Yanzu mutane na kaura zuwa garuruwan da suke ganin ya fi tsira. Muna bukatar sojoji don su kare mana wannan yanki."

Rundunar yan sanda ta yi martani

Da aka tuntube shi, jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Kebbi, DSP Nafiu Abubakar, ya ce zai kira baya idan ya samu cikakken bayani kan lamarin. Zuwa yanzu dai ba a samu ji daga gare shi ba.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Wani Kazamin Hari Jihar Arewa, Sun Kashe Basarake

Yan sanda sun damke wani mutum da makamai a Kaduna

A wani labarin kuma, rundunar yan sandan jihar Kaduna ta yi nasarar cafke wani mutum mai suna Bilyaminu Saidu dauke da bindigogin AK47 guda hudu da alburusai.

Matashin ya nado makaman ne a cikin wata buhu a kan babur dinsa tare da wani lokacin da yan sandan suka yi ram da shi, sai dai wanda suke taren ya tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel