Bishir Mangal, Shugaban Kamfanin Max Air, Ya Rasu A Abuja

Bishir Mangal, Shugaban Kamfanin Max Air, Ya Rasu A Abuja

  • Allah ya yi wa Alhaji Bashir Bara'u Mangal, mataimakin ciyaman kuma babban jami'in kamfanin Max Air rasuwa
  • Sanarwar da sashin watsa labarai na Max Air ta fitar ya ce Mangal ya rasu a ranar Juma'a 23 ga watan Disamba a Abuja
  • Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, ya yi ta'aziyyar rasuwar Mangal

FCT, Abuja - Mataimakin ciyaman kuma babban jami'i na kamfanin jiragen sama na Max Air, Alhaji Bishir Barau Mangal, ya riga mu gidan gaskiya.

Bishir, kanin babban dan kasuwa kuma ciyaman na Max Air, Alhaji Dahiru Bara'u Mangal, ya rasu ne a safiyar ranar Juma'a a Abuja.

Mangal
Bishir Mangal, Shugaban Kamfanin Max Air, Ya Rasu A Abuja. Hoto: Intel Region
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

2023: Sabon Rikici Ya Ɓalle, PDP Ta Dakatar da Kakakinta Na Jihar Arewa, Yace Ya Yi Murabus

Ya rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Wani majiya daga iyalan ya shaida wa Daily Trust cewa za a yi jana'izar marigayin a yau a garin Katsina misalin karfe 5 na yamma.

Hazalika, wata sanarwa da sashin watsa labarai na Max air ta fitar ya tabbatar da rasuwarsa.

Sanarwar ta ce:

"Inna lillahi wa inna Ilaihi rajiun, ana sanar da rasuwar dan uwa Alhaji Bashir Mangal, mataimakin ciyaman kuma CEO na Max Air da ya rasu da safiyar yau Juma'a 23 ga watan Disamban 2022. Allah ya ba shi aljanna Firdausi."

A cewar kamfanin, Mangal ya kasance gogaggen mai jagora kuma kwararren mai kula da mutane da albarkaru, sannan kwararren mai saka hannun jari kuma cikakken mutum wanda kai cika alkawari idan ya yi.

Atiku ya yi ta'aziyyar rasuwar Mangal

A sakon ta'aziyya da ya wallafa a Twitter, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya ce marigayin ya yi fice wurin gudanar da ayyukansa a kamfanin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Najeriya Ta Bada Hutun Kirsimeti Da Sabon Shekara

A cewar Atiku, Mangal yana da baiwar iya kasuwanci.

Hadimin Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

A wani rahoton daban, mashawarcin gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule kan ayyuka na musamman, Alhaji Murtala Lamus ya rasu a ranar 25 ga watan Oktoba.

Ibrahim Addra, babban sakataren labarai na gwamna Abdullahi Sule ne ya sanar da rasuwar Lamus a wata sanarwa da ya fitar kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel