Yadda Wani Ango Ya Mari Amaryarsa A Yayin Bikin Daurin Aure

Yadda Wani Ango Ya Mari Amaryarsa A Yayin Bikin Daurin Aure

  • A taron wani aure, anga wani ango ya mari matarsa a gaban wani malamin majami'a a cikin maja'mi'ar
  • Abinda ya farun na marin, wani wanda ya halarci daurin auren ne ya wallafashi a shafinsa na kafafen sadarwa
  • Mutanen na mamakin yadda wanan abun ya faru ko dai wani abu ne wanda ya faru da mutane basu gani ba

Aure dai wani abu ne da ake yinsa cikin farin ciki da annushuwa hadi da walwala, da ake gayyato 'yan uwa da abokan arziki dan suzo su sheda abun.

To sai dai a wannan fefan bidiyon ba abun haka yake ba, gani akai wani ango ya ware ya dallawa Amaryarsa mari.

A al'adar mabiya addinin kirista na yin aurensu a coci ko a kotu. Su kuwa musulmi na yinsa ne a masallaci ko kafar gidan waliyan amarya.

Kara karanta wannan

Bakon Biki Ya Gwangwaje Amarya da Ango da Daurin Itace, Bidiyon Ya Ba Jama'a Mamaki

Tik-tok
Yadda Wani Ango Ya Mari Amaryarsa A Yayin Bikin Daurin Aure Hoto: Tik-tok
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wannan bidiyon auren, an ga malamin majami'ar na umartar Ango ta Amarya su sumbaci junansu, amma anga ango ya mari matarsa. Kamar yadda @esthernice2 ta wallafa bidiyon

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin Masu Amfani Da Kafar Sadarwa.

Sashen Legit.ng na ingilishi ya tattaro bayanan mutane kamar haka:

TarlishaB yace :

"Gaskiya matar nan na cikin tashin hankali, indai zai mareta haka da wuri to ta kula"

Oluwadamilola yace:

"menene wannan?"

I am Trini yace:

"Inda al'ada ce to shiken, amma inda ba al'ada bace kawai shine ya aikata haka, to ya kamata ace malamin majami'ar ya bashi dama."

Jae Daniels yace:

"Yi hakuri, gaskiya na rasa wannan lokacin, inama zanga wannan abun da kuma yadda zai kasance"

Kara karanta wannan

Yadda Al'umma Suka Hadu Suke Gasar Cin Abinci a Jihar Cross - RIver

Queen Kemi tace:

"Shin Faston ne ya umarcin angon ya mareta, sabida yasan ya yanayin hakurinta yake, sabida wasu matan da yawa sun fi son tashin hankali"

Wata Amarya Ta Mari Angonta

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rawaito cewa wata amarya ta mari angota a wajen bikin aurensu.

A wani bidiyo da aka wallafa, mai tsawon dakika 19, anga amarya ta mari angonta, yayin da kowa yaki

A dalilin da ake tunanin angon ya tursasata taci kek din, ita kuma tayin kokarin ya tsaya amma yaki, shi kuwa ta mareshi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel