Wasu Ƴan Bindiga Sunyi Sanadiyyar Kashe Mutane Da Dama Akan Bazawararsu

Wasu Ƴan Bindiga Sunyi Sanadiyyar Kashe Mutane Da Dama Akan Bazawararsu

  • Garin Mutunji ya hadu da iftila'in da bai taba haduwa da irinsa ba, bayan da 'yan bindiga suka janyo musu ruwan wuta daga sama
  • Rikicin da ke tsakanin 'yan bindigar ne ya janyo kaiwa garin Mutunji hari inda suka rasa mutanensu da dama yayin da wasu suka tsira da raunuka.
  • Jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi da katsina har ma da Kaduna na fama da matsalar 'yan bindigia masu sace mutane dan kudin fansa.

Zamfara: Garin Mutunji a jihar zamfara ya hadu da iftila'in da bai taba haɗuwa da irinsa ba. Ana fargabar mutane sama 64 ne suka rasa ransu kamar yadda kafar BBC Hausa ta rawaito.

Inji wani mazaunin gatin da yake zantawa da BBC Hausa yace:

"Anyi asarar rayukan da ba a taɓa samu ba, kuma ga wasu da yawa sun jikkata."

Kara karanta wannan

Babbar Nasara: Ƙasurgumin Ɗan Bindigan da Aka Fi Nema Ruwa a Jallo Ya Shiga Hannu

An Caskale Akan Bazawara

Mazauna garin Mutunji sunce kaman sati guda da ya shude an samu saɓani tsakanin rukunin ƴan bidiga guda biyu akan wata bazawarsu. A dalilin wannan hatsaniyyar wasu daga cikin ƴan bindigar sun rasa ransu. Babban dan bindigan daga ɗaya tsagin da sukai fadan yace ai mutanen gari ne suka kashe masa yara, dan haka sai ya dau fansa, in ji wani mazaunin garin da yake bayar da ba'asin yadda abun ya faru. Bayan gano ba mutan gari bane suka aikata wannan mummunan illar sai shugaban ƴan bindiga din ya kaiwa waɗan can tsagin hari, haka kuma yasa sojoji suka ziyarci yanki a hanyarsu ne ta zuwa ƴan bindigar sukai musu kwantan Ɓauna suka kashe tara daga cikinsu. Bayan aika-aikar da waɗan ƴan bidigar sukai sai suka shige garin Mutunji dan neman mafaka hakan kuma yasa sojoji suka kai hari ta jirgin saman garin, inda mutum 69 suka rasa ransu. Kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Bankawa Babbar Kotun Jiha Wuta, Sun Tafka Ɓarna

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Zawarawa
Wasu Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama Akan Bazawararsu Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Me sojoji suka ce?

Jaridar PRNigeria tace wata majiyar sirri ta fada mata yadda dakarun sojin sukai kai hari kan ƴan bindigar

To sai dai bayan fara kai harin ne wasu ƴan bindigar tserewa zuwa ga garin mutu ji. Bayan da sojiji suka samu tabbacin baza su taba kowa ba sai suka sakar musu bam.

A wannan dalili akai hasarar dukiya da rayukan al'ummar garin Mutunji da kuma ƴan bindiga guda 40, kamar yadda rahotan PRNigeria yace.

Wasu mutanen kauyen da ke kusa da garin Mutunji sun yaba da kai harin tare da yin alhinin wanda harin ya shafa nada cikin fararen hula.

Asali: Legit.ng

Online view pixel