Takaitaccen Tarihin Wani Mamaci da 'Ya'yansa Suka Rubuta Ya Ba Mutane da Yawa Mamaki
- Takaitaccen tarihin wani mutumin da ya mutu kuma 'ya'yansa suka rubuta ya yadu a kafar sada zumunta, mutane na ta cece-kuce
- Mutumin mai suna Cif Gabriel Osonwa Kalu ya rasu yana da shekaru 66, kuma 'ya'yansa sun bayyana bai tsinana musu komai ba
- Wani daga cikin 'ya'yan nasa da ta rubuta takaitaccen tarihinsa ya ce tabbas yana matukar dana-sanin kasancewa dansa
Mutane a kafar sada zumunta sun shiga mamaki bayan ganin wani hoto na yawo na tarihin wani mamaci dan Najeriya da ya rasu yana da shekaru 66.
Samuel Strong ya yada tarihin mutumin a shafin jama'a na Facebook mai suna Rant HQ Extention, inda yace tuni suna binne mutmin
'Ya'yan mutumin da suka amince tabbas babu wanda ya kuskure a duniya, sun koka a nasu bangaren da cewa, mutumin bai tsinana musu komai ba.
Marubucin tarihin dattijon ya ce yana matukar dana-sanin kasancewa dan mamacin lokacin da ya taso a gidansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Ya'yan sun kuma bayyana mahaifinsa a matsayin mai haba-haba da wasu mutane na waje, amma ya yi biris da danginsa.
Ga kadan daga abin da suka rubuta:
"...Tabbas ka kasance mai alheri ga bare amma a gida kuma ka kasance makwaloto. Yayin da nake girma, na yi dana-sanin kasancewarka mahaifina, amma a yau, kalle ni, ina tsaye domin binne ka a makwancinka."
Martanin jama'ar Facebook
Isaac Inwang:
"Idan Allah ya ba di nisan kwana haka, kada Allah ya sa 'ya'ya na su siffanta ni ta yadda aka siffanta wannan mutumin."
"Allah yasa 'ya'ya na su yi murnar kasancewa ta ubansu a rayuwata da mutuwa ta."
Charles Ndubuisi:
"Ni dai ina da mahaifi abin alfahari da kowa ke bukatar kamarsa amma ko da akasin haka na samu ba zan muzanta suna da tarihinsa kamar haka ba."
Awang Patrick:
"Ban ga laifinsu ba ko kadan...Na san zafin samun uban da bai damu da 'ya'ya ba wanda shaidan ne a gida amma mala'ika a waje...Hakan ya faru dani..."
Adebayo Bello:
"Wannan ne babban sako ga 'ya'yan masu kudin da ba sa haba-haban neman na kansu amma suke sanya tunaninsu kan gado. Wannan kenan abin da ubayenku za sui muku."
Cynthia Michael Okpamen:
"Ubanni dai haka suke, Gwanaye a waje amma mugaye ga na gida. Idan ka gaza a wajen 'ya'yanka a matsayin uba to kada ka tsammance soyayya ko bayan mutuwa.
"Iyeye kuke yin aikinku kamar ba za ku rabu da 'ya'yanku ba. Cewar ka yi sa'an samun uba na gari ba yana nufin wani ma haka bane."
Kwanakin baya Ali Nuhu kuwa ya yada hotuna n dansa, yace yana alfahari dashi bisa abubuwan da yake yi.
Asali: Legit.ng