Wani Magidanci Ya Kama Matarsa Tana Almubazzaranci Da N5m Da ya Bata Dan Fara Kasuwanci

Wani Magidanci Ya Kama Matarsa Tana Almubazzaranci Da N5m Da ya Bata Dan Fara Kasuwanci

  • Wani magidanci ya kama matarsa ​, kuma ya nemi ta yi masa bayanin yadda ta wofantar da kudin da ya bata har Naira miliyan 5 dan ta fara kasuwanci
  • A wani faifan bidiyo da Rita4Delta ta wallafa a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba, an ga matar ta kasa yin lissafin kudin da ya bata bayan watanni uku
  • Masu amfani da TikTok sun kadu da labarin yayin da suke ƙoƙarin fahimtar yadda mutum barnatar da wannan kudin adadin cikin kankanin lokaci

Masu amfani da TikTok sun yi matukar kaduwa da labarin wata mata da ta yi almubazzaranci da kudaden da suka kai Naira miliyan 5 cikin watanni uku.

An ba da labarin matar ne a wani faifan bidiyo da aka wallafa a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba, ta Rita4Delta wadda ta ce ta san matar da ake maganar ta ta.

Kara karanta wannan

Ki sauka kawai: Dirama ta barke, kwandastan bas ya ki karban N100 sabuwar bugu

A cikin faifan bidiyo na mintuna 3 , Rita ta bayyana cewa matar ta kasa lissafa abubuwan da tayi da kuɗin.

Magidanci
Wani Magidanci Ya Kama Matarsa Tana Almubazzaranci Da N5m Da ya Bata Dan Fara Kasuwanci Hoto: Getty
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Labarin matar da ta salwantar da Naira miliyan 5 a cikin wata uku

Ta ce an bai wa matar kudin ne domin ta fara kasuwancin sai da giya , kuma kasuwancin bai je ko'ina ba ya dakushe.

Sakamakon kasa bayyana abin da ya faru, mijin matar ya kaita wajen ‘yan sanda.

A yanzu dai bidiyon da aka wallafa ya samu masu sharhi da goyan bayansu akansa kusan mutum dubu uku.

Kalli bidiyon a kasa:

Martani daga masu amfani da TikTok

@augusta Eromosele ya ce:

"wannan shari'a ce ta wanda ya samu dama bai yi amfani da ita ba ko kuma wanda ya samu dama ya watsar da ita"

Kara karanta wannan

2022: Mai Kamfanin BUA Ya Samu Cigaba, Shine na 4 a Jerin Masu Arzikin Afrika

@chigozieduru6 yace:

"Ya kamata mijin matar nan ya samu bayanan hada-hadar bankinta, domin ya tabbatr ba wani saurayin take turawa kudin ba."

@Godswill Igwe862 a nasa sharhi ya ce:

"Allah ya sa bazan dauko cuta da hannu na ba (muguwar mata) wahala."

@Emily Edward635 ta mayar da martani:

"Akwai mutumin da na sani yaje ya kaiwa bankin bada rance na LAPO yace matar taje can ta karbo kudin sabida yasan halinta dana yan uwanta"

Wata Matar Aure Ta Samu Ciki Da Direbanta

A wani labarin mai kama da wannan, Legit.ng ta ruwaito cewa, wata mata ta samu ciki da wani mutum a wanda ba mijinta ba.

Matar ta furta a cikin wani faifan bidiyo cewa ta kwanta da direbanta sau biyu kuma ta samu ciki.

Masu amfani da shafukan sada zumunta da suka mayar da martani ga labarin sun kadu matuka.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel