Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno Ya Rasa 'Ya'Yansa Biyu a Hatsari

Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno Ya Rasa 'Ya'Yansa Biyu a Hatsari

  • Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Hon Inuwa Kubo, ya yi rashin 'ya'yansa guda biyu a hatsarin mota
  • Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya rutsa da su ne a kan hanyar zuwa taron kamfe a ƙaramar hukumar Shani da yammacin Laraba
  • Tuni dai aka musu Jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada da safiyar Alhamis

Borno - Tsohon kwamishinan Ilimi kuma tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Hon Inuwa Kubo, ya yi rashin 'ya'yansa guda biyu, Adamu da Audi a wani mummunan hatsarin mota.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa bayansu, wasu mutum biyu sun mutu a hatsarin wanda ya auku a Titon Kwaya-Kusar- Peta- Shani da yammacin ranar Laraba.

Hon Inuwa Kubo.
Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno Ya Rasa 'Ya'Yansa Biyu a Hatsari Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

An tattaro cewa suna cikin tafiya motarsu ta kucce wa mai tuƙin ta bugi Tulin yashi da masu aikin kwangila a babban Titin suka tara.

Kara karanta wannan

'Muna Bukatar Tinubu Fiye da Yadda Yake Bukatar Mu a 2023', Jigon siyasa

Vangaurd tace lamarin ya rutsa da su ne a hanyar zuwa ƙaramar hukumar Shani daga Maiduguri domin halartar gangamin yakin neman zaɓen APC wanda mataimakin gwamna zai kaddamar ranar Alhamis a mazabar Borno ta kudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A halin yanzun baki ɗaya mamatan an musu Jana'iza kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada bayan gari ya waye ranar Alhamis.

Sakamakon haka, Mataimakin gwamnan Borno, Hon. Umar Usman Kadafur, ya soke kamfen kana ya bi Jirgin Helikwafta ya halarci Jana'iza tare da yi wa iyalai ta'aziyya.

Ya kuma roki Allah ya sa Aljannatun Furdausi ta zama makoma a garesu, ya gafarta masu kura-kuransu, ya karbi ayyukansu na kwarai. Iyalansu kuma Allah ya basu hakuri.

Mutanen da suka je ta'aziyya tare da Kadafur

Yayin ziyarar jaje, Kadafur ya samu rakiyar Sanatan Kudancin Borno, Ali Ndume, da kakakin majalisar dokokin jihar, Rt.Hon.Abdulkarim Lawan.

Kara karanta wannan

2023: "Ka Ci Zaɓe Ka Ci Zabe" Yadda Dubun Dubatar Magoya Baya Suka Yi Maraba da Tinubu a Jihar Arewa

Sauran sun haɗa da ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Gwoza, Chibok da Damboa, Hon. Ahmed Jaha Babawo, da takwaransa mai wakiltar Hawul/ Askira-UBA, Dr Haruna Mshelia, da wasu jiga-jigan APC.

Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ya Murkushe Wata Mota

A wani labarin kuma Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya murkushe wata Mota da ke kokarin tsallaka titinsa a kusa da tashar kubwa

Wasu Hotun da suka karaɗe kafafaen sada zumunta sun nuna yadda mutane suka kewaye wurin domin kai ɗaukin gaggawa.

Sai dai babu tabbacin ko an rasa rai sakamakon lamarin zuwa yanzu, kusan mako biyu kenan da dawowar aikin jirgin kasan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel