Nigeria da Wasu kasashen Duniya Na Fama Da Katutun Bashi

Nigeria da Wasu kasashen Duniya Na Fama Da Katutun Bashi

  • Bankin Duniya ya gargadi Nigeria akan yadda tattalin arzikinta yake tangal-tangal
  • Ya Kamata Nigeria ta shiga taitayinta, game da tulin basussukan da suke kanta kamar yadda babban bankin Duniya ya sanar
  • Basukan da suke damun Nigeria kan iya janyo mata karyewar darajar kudinta hadi da tashin kudaden waje inji masana

Bankin Duniya ya ce Nigeria da sauran kasashe masu tasowa na fuskantar matsalar basussuka, inda ya ce lamarin ya kara kamari.

Shugaban Bankin Duniya, David Malpass, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Biyan Bashi Da Hidindimun Dake Tattare Dashi Yasa Kasashe Fad'awa Halin Kunci Da Talauci Tun 2000’.

A cewar Bankin Duniya, sabon rahotonsa na bashi wanda ya fitar kan kasa da kasa ya bayyana hadarin da ke da nasaba da bashi ga kasashe masu tasowa da wanda suke da karamin karfi da kuma masu matsakaicin tattalin arziki.

Hoto: Babban Banki
Nigeria da Wasu kasashen Duniya Na Fama Da Katutun Bashi The Punch
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar The punch tace lokacin da baban manajan babban bankin ke tofa albarkacin bakinsa, Malpass ya ce,

“Rikicin bashi da kasashe masu tasowa ke fuskanta ya karu. Ana buƙatar cikakkiyar hanyar rage basussuka, da kuma sauƙaƙe yadda suke kashe kuɗi wanda a ke basu dan rage talauci".
"Idan ba tare da bashi ba, kasashe da yawa baza su iya warware kasafin kudinsu ba, har ma su samu damar da zasu magance wasu matsaltsalun da suka addabesu". Inji Malpass

Bankin da ke da hedikwata a Washington yace wasu daga Ƙasashen Duniya a yanzu sun kashe sama da kashi goma na kudaden da ake basu lamuni daga asusun da gwamnatin ta ke ware musu.

Ya ce a karshen shekarar 2021, bashin da ake bin wadannan kasashe ya kai dala tiriliyan 9, wanda ya ninka adadin shekaru goma da suka gabata tare da jimillar bashin kasashen IDA wanda ya kusan ninkawa sau uku.

Malpass Ya ce,

"Yadda ake samun karin ruwa yana jefa ƙasashen cikin rikicin bashi. Kusan kashi 60 cikin 100 na kasashen matalauta ne da sun riga sun fada hadarin bashi da halin kunci".

Rahotan ya tabo batun yadda kasashen duniya ke kin biyan bashi da hatsarinsa, inda rahotan yace:

"A karshen shekarar 2021, kasashen da ya kamata ace sun biya bashin da ke kansu basu biya ba wanda an samu karin kudin ruwa kusan kashi 46.2, kwatankwacin kashi 10.3 na kudin shigarsu, a cewar rahoton.”

Hakazalika, rahoton ya gargadi gwamnatin tarayya kan yin watsi da sashe na 38 na dokar CBN, wanda ya kayyade rancen da bankin zai yi zuwa kashi 5 na kudaden shiga na kudin kasa.

Gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da babban bankin Najeriya ya ba gwamnatin tarayya bashin da ya haura N22tn.

Me Yasa Gwamnatin Nigeria Cin Bashi

A cewar ofishin kula da basussuka, abubuwa da yawa ne ya sa gwamnatin tarayya ta ciyo rancen kudi daga bankin CBN.

Gwamnatin taci bashin da yakai N17.46tn wanda taci a watan Disambar 2021. Zuwa yanzu kuwa gwamnatin tarayyar taci bashin da yakai N23.77tn zuwa karshen watan Oktoban 2022.

A halin da ake ciki gwamnatin ta karbo rance daga bankin CBN wanda kuma ya sabawa sashe na 38 na dokar CBN na shekarar 2007, inda bashin ya zarce ka’idojin da doka ta tanada akan irin wannan rancen.

Dokar ta kara da cewa,

“Jimillar kudaden da aka samu ba za su wuce kashi biyar cikin dari na ainihin kudaden shigar gwamnatin tarayya na shekarar da ta gabata ba a kowane lokaci.”

Wani bangare na rahoton ya kara da cewa,

“Hanyoyi samar da kudade daga CBN na raguwa yayin da kudin da ake kashewa wajen biyan kudin ruwa kuma na karuwa.”

Wani masanin tattalin arziki Dakta Aliyu Iliyas, ya soki gwamnati kan yadda take dogaro da rance a kullum, wanda hakan ba shi da alfanu ga tattalin arzikin kasar.

Ya bukaci gwamnati da ta nemi ingantattun hanyoyin samun kudaden shiga maimakon ci gaba da karbar rance daga babban bankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel