Majalisar Dokokin Indonesiya Ta Amince Da Haramta Jima'i Kafin Aure

Majalisar Dokokin Indonesiya Ta Amince Da Haramta Jima'i Kafin Aure

  • Kasar indonosiya da take yankin arewa wacin nahiyar Asia, wanda mafi yawansu mabiya addinin musulunci ne
  • Majalissar Dokokin Kasar ta tayi doka kan hana duk wani abu na mu'amala tsakanin mace da miji wanda ya shafi aure har sai bayan anyi
  • Dokokin da majalissar ta sanya dai yan kasar da kuma masu rajin kare hakkin dan adam sunce sunyi tsauri

Indonosiya - A jiya Talata Majalisar dokokin kasar Indonesiya ta amince da dokar haramta yin jima'i ba tare da aure ba,. A wani mataki da masu sukar lamarin da suke cewa wani babban koma baya ne ga hakki 'Dan-adam.

Bayan amincewa da sabon kundin tsarin laifukan da dukkan jam’iyyu tara na kasar suka yi, a wani gagarumin gyara kan kundin dokokin kasar, a wani rahoton Channels Tv

Mataimakin kakakin majalisar Sufmi Dasco Ahmad ya rattaba hannu yana nuna cewa an amince da batun kuma hakan na nuna 'wannan doka ne'.

An shafe shekaru da yawa ana muhawara kan sake fasalin kundin laifuka na kasar ta Indonesiya, wanda ya fara tun zamanin mulkin mallaka.

indonosiya
Majalisar Dokokin Indonesiya Ta Amince Da Haramta Jima'i Kafin Aure Hoto: IMA
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da sauye-sauyen.

Inda suka yi tir da yadda aka murkushe 'yancin jama'a da 'yancin siyasa, da kuma koma-bayan bayyana ra'ayi a kasar Indonesiya mai rinjayen musulmi, inda aka sanya tsarin mulkin addini a cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Ministan shari'a da kare hakkin bil'adama, Yasonna Laoly ya shaidawa, majalisar dokokin kasar cewa:

"Mun yi iya kokarinmu don ganin mun daidaita muhimman batutuwa da kuma ra'ayoyi daban-daban da aka yi muhawara a kai kafain yanke hukuncin."

"Ministan ya kara da cewa, lokaci ya yi da za su yanke hukunci game da gyaran dokar laifuka da kuma barin kundin laifukan mulkin mallaka da suka gada."

Kungiyoyin kasuwanci na kasar ta Indonesiya sun soki lamarin da cewa aikata laifin yin jima'i ba tare da aure ba zai cutar da baki masu yawon bude ido, duk da cewa hukumomi sun nace ba zai shafi baki da ke tafiya zuwa kasar ba.

Sabon kundin wanda har yanzu yana bukatar amincewar shugaba Joko Widodo, zai fara aiki ne bayan shekaru uku.

Shekara Daya a Gidan Yari

Wasu labaran da suka fi jawo cece kuce a cikin sabon kundin sune haramta yin jima’i da yawa, da kuma zaman tare da tsakanin namiji da mace ba tare da sunyi aure ba.

Rahotanni na nuna cewa, za a hukunta wanda ya aikata laifin jima'i ba tare da aure ba da zaman gidan yari na tsawon shekara guda, yayin da wadanda ba su da aure da ke zaune tare za su fuskanci zaman gidan yari na watanni shida.

Albert Aries na ma'aikatar shari'a da kare hakkin bil'adama ya kare gyare-gyaren dokar kafin kada kuri'ar, kuma ya ce dokar za ta kare cibiyoyin aure.

Ma'aurata, iyaye ko 'ya'ya ne kawai za su iya ba da rahoton jima'i a ba tare da aure, tare da iyakance iyakar gyaran, in ji shi.

A wani taron kasuwanci gabanin kada kuri'a a ranar Talata, jakadan Amurka a Indonesia Sung Yong Kim ya ce ya damu da ka'idojin aikata laifuka da za su iya yin tasiri kan kasuwanci.

Sannan ya magantu kan yadda za'a bawa masu ra'ayin auren jinsi dama, da kuma wanda suke da wani abu makamancin cudanya da juna ko akasin haka

A Mataki Baya: Manazarta sun ce Sabuwar kundin dokar zata tauye wasu haƙƙoƙin siyasa.

Hukuncin kisa da aka fi amfani da shi a kasar Indonesiya bisa laifukan safarar muggan kwayoyi, yanzu zai zo ne da sigar daurin tsawon shekaru 10 tare da yunkurin kasar na sauya wanda aka kama hali zuwa na kwarai.

Bambang Wuryanto, shugaban hukumar da ke sa ido kan shawarwarin dokokin, ya yarda cewa

"Wannan dokar batu ne da zai shafi mutane da dam wanda dole sai anyi taka tsantsan".

Wuryanto ya bukaci masu masu sukar da su kalubalanci abun a kotu ko kuma su sanar da shirya muhawarar jin bahasin batun

Kungiyoyin Kare Hakkin Sun Yi Tir Da Dokar.

Shugaban kungiyar Amnesty International ta Indonesia Usman Hamid ya shaida wa :

"Kaddamar da kudirin dokar aikata laifuka wani mataki ne na baya-bayan nan wajen kare hakkin jama'a, musamman kan 'yancin fadin albarkacin baki da 'yancin yada labarai".

Yunkurin zartar da daftarin doka makamancin haka a shekarar 2019 ya jawo dubun-dubatar mutane fitowa kan tituna a zanga-zangar da a karshe ta tilastawa gwamnati ja da baya.

A ranar Talata kusan masu zanga-zanga goma ne suka taru a cikin garin Jakarta rike da tutoci. da kwalaye wanda ke dauke da rubutun:

"Kun sake amfani da dokar zamanin mulkin mallaka, .

"Ta yaya zakai amfani da dokar mulkin mallaka?"

Asali: Legit.ng

Online view pixel