Yadda Wani Direban Tasi Ke Samun Makudan Kudade Kasar Qatar

Yadda Wani Direban Tasi Ke Samun Makudan Kudade Kasar Qatar

  • Wani dan Ghana mazaunin Qatar ya bayyana cewa yana samun sama da GH¢16,000 duk wata a matsayin direban tasi
  • A wata hira da aka yi da shi, Papa Kumasi ya tuna cewa yana aiki a masana'antar sufuri da kawata a Ghana kafin ya koma kasar Larabawa
  • Dan asalin yankin Akim Oda da ke Gabashin Ghana ya bayyana cewa ya shafe shekaru bakwai yana aikin tukin tasi a Qatar.

Wani dan Ghana mazaunin kasar Qatar da ake kira Papa Kumasi ya bayyana cewa yana samun sama da dirhami 16,000 duk wata a matsayinsa na direban tasi a kasar.

Da yake magana da mawallafin shafin yanar gizon Zionfelix, wanda kuma legit.ng ta rawaito, cewa: Papa Kumasi ya bayyana cewa ya yi aiki wani kamfanin gini a Ghana kafin komawarsa matsayin direban tasi.

Kara karanta wannan

Ko Me Ya Yi Zafi? Ɗan Najeriya Ya Yi Wa Budurwarsa Yankar Rago a Kasar Waje

Zionfelix TV
Yadda Wani DIreban Tasi Ke Samun Makudan Kudade Kasar Qatar Hoto: Zionfelix TV
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Me yasa Nayanke shawarar ƙaura zuwa Qatar

Ya kara da cewa ya yanke shawarar komawa kasar Qatar ne bayan abokansa sun sanar da shi cewa zai iya samun fiye da ninki biyu kudin na kudin da yake samu a Ghana.

Dan asalin yankin Akim Oda da ke Gabashin kasar Ghana ya bayyana cewa ya shafe shekaru bakwai yana aiki a fannin sufurin kasar Qatar.

Papa Kumasi ya shaidawa Zionfelix cewa ya isa kasar Larabawa ne tare da taimakon wani wakili kuma ya samu lasisin tuki a makarantar tuki, inda ya ci jarrabawar sa bayan gwadashi da sukai.

Albashin Papa Kumasi da sauran Abubuwan da Ya Ke Samu

Ya bayyana cewa yana aiki awanni 10 a kullum na tsawon kwanaki shida a kowane mako, tare da samun wasu fa'idoji daga kudin wanda suka hada da na kiwon lafiya.

Kara karanta wannan

Abu Mai Sosa Zuciya: Hotunan Wani Matashi Bai Ci Abinci Ba Tsawon Kwana 2 ya Samu Taimako

Na fara da samun dirhami 4,776.33 amma yanzu yana ɗaukar dirhami 4,200 kamar , ya gaya wa Zionfelix.

Lauya A Najeriya Yana Samun N10k da Tasi Kullum

A wani labarin mai kama da haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa wani lauya dan Najeriya mai shafin Twitter @AlamsKabuk ya bayyana yadda yake samun N10,000 a rana daya daga aikin tasi.

Ya ce ribar da ya ke samu ya sa ya yi tunanin barin aikin lauyansa ya zama direban dan ganin ya fi gwabi.

Mutumin ya kara da cewa sai da ya yi amfani da Naira 1,000 daga cikin kudin wajen shakatawa bayan kammala aikin ranar. Lauyan ya bayyana cewa ya yi farin ciki da samun wannan abun

‘Yan Najeriya sun mayar da martani sosai a shafinsa na Twitter yayin da mutane suka tabbatar da cewa lallai akwai makudan kudade a harkar sufuri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel