Saboda Tsabagen Girmamawa, An Sanyawa Titi Sunan Muhammadu Buhari a Kasar Waje

Saboda Tsabagen Girmamawa, An Sanyawa Titi Sunan Muhammadu Buhari a Kasar Waje

  • Mutanen Jamhuriyyar Nijar sun tabbatar da irin soyayyar da suke yi wa Muhammadu Buhari
  • Yayin da Muhammadu Buhari yake halartar taron AU, an nadawa wani titi a Niamey sunansa
  • Malam Garba Shehu yace hakan ba komai ba ne illa girmamawan da ake yi wa shugaban kasar

Niger - Matukar girmamawan da suke yi wa shugaban Najeriya, ya jawo makwabciyar kasar daga Arewa watau Nijar, ta karrama Muhammadu Buhari.

Premium Times ta rahoto Malam Garba Shehu yana cewa an gina titi a birnin Niamey da ke Jamhuriyyar Nijar, an sa wa titin sunan shugaban Najeriya.

Mai ba shugaban kasar shawara wajen yada labarai ya bayyana wannan ne kasar Nijar, jim kadan bayan Muhammadu Buhari ya kaddamar da wannan titi.

Fadar shugaban kasar ta nuna jin dadinta kan irin alakar da ke tsakanin Najeriya da makwabtanta, tace wannan ya taimaka wajen yakar ta’addanci a yankin.

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Tinubu ya fadi yadda zai yi da 'yan IPOB idan ya gaji Buhari a 2023

Babu mamaki... - Garba Shehu

Garba Shehu yake cewa daga shigan Muhammadu Buhari ofis a 2015, ya zauna da kasashen Benin, Chad, Kamaru da Nijar, kuma hakan ya haifar da ‘da mai ido.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hadimin yace kokarin da Shugaba Buhari ya yi, ya taimaka sosai wajen magance matsalolin tsaro, fasa-kwauri, shigo da miyagun makamai da dai sauransu.

Titin Buhari
Titin Buhari a Niamey Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Malam Shehu yana sa rai wanda zai gaji mulki daga hannun Muhammadu Buhari a Mayun 2023, ya daura daga inda ya tsaya domin alakar kasashen ta daure.

Kamar yadda Shehu ya fada a ranar Alhamis, Mai girma Muhammadu Buhari ya cancanci a radawa titi sunansa saboda yadda mutanen Nijar ke karrama shi.

Mohammed Bazoum ya yi yawa da takwaransa

Shugaban Jamhuriyyar Nijar, Mohammed Bazoum da Shugabar birnin Niamey suka zagaya da Buhari yayi da ya kaddamar da titin mai tsawon kilomita 3.8.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Shugaba Muhammadu Buhari Zai Sake Tafiyar Kasar Waje Gobe

Yanzu haka Buhari da wasu shugabannin kasashen Afrika suna babban birnin Niamey domin halartar taron kungiyar AU da ake yi a kan tattalin arziki.

Wannan karramawa da shugaban ya samu ta zama ribar kafa yayin da yake halartar wannan taro. Bashir Ahmaad ya tabbatar da wannan labari a shafinsa.

Rabon aiki a NEITI da NUPRC

Za a binciki abin da ke faruwa a hukumomin NUPRC da NEITI a Majalisar Wakilan Tarayya, rahoto ya nuna korafin da jama’a ke yi ya jawo wannan bincike.

‘Dan majalisar Kano, Hon. Hafizu Ibrahim Kawu yace hukumomin nan sun dauki ma’aikata ba tare da sun yi adalci wajen rabon ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel