Gwamnan Imo Ya Fusata, Ya Tsige Shugaban Jami'ar Jiharsa Daga Mukaminsa

Gwamnan Imo Ya Fusata, Ya Tsige Shugaban Jami'ar Jiharsa Daga Mukaminsa

  • Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya sauke shugaban jami'ar Noma da Kimiyyar Mahalli ta jiharsa daga kan kujerarsa
  • A wata sanarwa da Sakataren gwamnatin jihar ya fitar, tace gwamnan ya amince da naɗa Farfesa Chiedozie Eze a matsayin mukaddashin VC
  • Sanarwan ta yi wa tsohon VC fatan alheri yayin da ta bukaci wanda aka naɗa ya tashi tsaye wajen gina makarantar mai taso wa

Imo - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya tsige shugaban jami'ar koyon Noma da Kiwo da Kimiyyar Muhalli ta jihar dake Umuagwo, (VC), Farfesa Patrick Egbule.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Gwamna Uzodinma, ya tunɓuke Farfesan daga kan muƙaminsa ne a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ranar Laraba a Owerri.

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.
Gwamnan Imo Ya Fusata, Ya Tsige Shugaban Jami'ar Jiharsa Daga Mukaminsa Hoto: Hope Uzodinma
Asali: UGC

Sanarwan wacce ta fito daga Ofishin Sakataren gwamnatin jihar, Cosmas Iwu, ta ce an maye gurbin Farfesa Egbule da Farfesa Christopher Chiedozie Eze a matsayin mukaddashin VC na jami'ar.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso Ya Ɗebo Ruwan Dafa Kansa, Na Hannun Daman Atiku Ya Maida Masa Martani

Punch ta rahoto Wani sashin sanarwan ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mai girma zaɓaɓɓen gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya amince da sauke Farfesa Patrick Egbule daga kujerar shugaban jami'ar koyon aikin Noma da Kiyo da Kimiyyar Mahalli ta jihar Imo da ke Umuagwo."
"Bayan haka kamar yadda dokar kafa jami'ar ta tanaza Mai girma gwamna ya amince da naɗin Farfesa Christopher Chiedozie Eze a matsayin shugaban riko na jam'iyyar Noma da Kimiyyar Mahalli ta jiha."

Gwamna ya yi wa tsohon VC fatan Alheri

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa gwamnan ya yi wa tubabben VC fatan Alheri a dukkanin lamurran da zai fuskanta na gaba, ya kuma gargaɗi sabon ya tashi tsaye.

"Yayin da gwamna ke wa tsohon muƙaddashin VC fatan Alheri a dukkanin abubuwan rayuwa nan gaba ya kuma buƙaci sabon, Chiedozie Eze, da ya sa kansa ta yadda zai ɗaga darajar makarantar mai taso wa."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Na Hannun Daman Buhari Ya Shiga Kungiyar Gwamnonin G5, Ya Kulla Yarjejeniya Da Wike

- A cewar sanarwa daga gwamnatin jihar Imo.

A wani labarin kuma Ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa ASUU tace zata ɗauki mataki Matukar gwamnatin Buhari ta gaza biyansu Albashin watannin yajin aiki

Malaman sun yi barazanar tsallake zangon karatun da aka yi yajin aiki matukar FG ta kafe kan bakarta na 'Ba aiki ba albashi' na waɗannna watannin.

Wasu malaman jami’ar UNIPORT sun ce sam dazata sabu a hana su hakkokinsu ba tun da duk tsayin yajin aiki idan aka janye suna biyan karatun baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel