Kada Ku Yarda Da Wadanda Suka Rainawa Kiristoci Hankali, Atiku Ga Jama'ar Benue

Kada Ku Yarda Da Wadanda Suka Rainawa Kiristoci Hankali, Atiku Ga Jama'ar Benue

  • Gabanin zaben 2023, dan takarar kujerar shugaban kasan Peoples Democratic Party (PDP) ya roki al'ummar Benue
  • A jihar Benue, ya roki al'ummar su daina yi masa kallon Fulani, amma halastaccen dan Najeriya
  • Ya bayyana cewa gwamnatinsa zata dama da kowa, Musulmi ko Kirista kuma za'a girmama doka

Mkar - Dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya bayyana muradunsa ga al'ummar jihar Benue.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, wanda ya bayyana hakan ranar Alhamis, 17 ga Nuwamba a taron cocin 82nd Synod of the Universal Reformed Christian Church, aka NKST, a Mkar, jihar Benue ya ce zai cigaba da kasancewa tare da al'ummar Benue kamar yadda yayi a baya.

Atiku
Kada Ku Yarda Da Wadanda Suka Rainawa Kiristoci Hankali, Atiku Ga Jama'ar Benue Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Depositphotos

Atiku wanda ya samu wakilcin Farfesa Iorwuese Hagher da Hanarabul Chille Igbawua na kwamitin kamfen PDP, yace:

Kara karanta wannan

2023: Ku Yi Hattara Da Peter Obi, Kungiyar Matasan Kirista Ta Aike Da Sako Mai Karfi Ga Yan Najeriya

"Jam'iyyata PDP mai hankali ce ga rabon mulki tsakanin Kiristoci da Musulmai a kasar nan."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Wadanda suka ki girmama addininmu sun yi hakan ne da gayya. Ba zamu bari su tsira ba."

Atiku Yace al'ummar Benue su zabesa

Atiku ya yi kira da jama'ar Benue su daina yi masa kallon Fulani amma a matsayinsa na Atiku Abubakar.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, ya yi waiwaye kan rawar da ya taka lokacin rikicin Zaki-Biam da Gbeji da Adoor kuma yadda ya tsaya da al'ummar Benue.

Yace:

"Mun shiga lungu da sakon Zaki-Biam ranar da abin ya faru, mun yi Alla-wadai da kisan al'ummar Tibi kuma an ga gaskiyarmu daga baya lokacin Soji suka bada hakuri."
"Har yanzu ni ne Zege Mule u Tiv, ina tabbatar muku cewa idan kuka zabeni matsayin Shugaban kasa, babu dan Najeriyan da zai gaza bacci saboda yan ta'adda."

Kara karanta wannan

Kwanaki Kadan Bayan Kaddamar da Kamfe, Bola Tinubu Ya Yi Gagarumin Rashi a Jihar Arewa

Zamu Baka Kuri'u Miliyan Biyu a Zaben 2023, Yan PDP A Jos Sun Yi Atiku Alkawari

A wani labarin kuwa, yan Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Plateau sun yiwa Alhaji Atiku Abubakar alkawarin kawo masa kuri’u miliyan biyu a zaben 2023.

Jiga-jigan jam’iyyar a jihar sun bayyana hakan ne a yayin bikin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben Atiku-Mutfwang a Jos, babban birnin jihar

Asali: Legit.ng

Online view pixel