2023: Dubban ‘Ya’yan Jam’iyyar APC Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Sokoto

2023: Dubban ‘Ya’yan Jam’iyyar APC Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Sokoto

  • Yan kwanaki bayan kaddamar da yakin neman zabenta na shugaban kasa, jam'iyyar APC ta yi babban rashi a jihar Sokoto
  • Mambobin APC kimanin su 2,343 sun fice daga jam'iyyar mai mulki inda suka koma jam'iyyar Atiku Abubakar
  • Da yake tarban masu sauya shekar, dan takarar gwamnan PDP a jihar Sokoto, Mallam Saidu Umar, ya dauki alkawarin tafiya da su a duk wasu harkokinsa

Sokoto - Dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Sokoto, Mallam Saidu Umar, ya tarbi mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) 2,343 zuwa cikinsu.

Dubban magoya bayan na APC sun sauya sheka zuwa babbar jam’iyyar adawar ne a yankin Mainiyo da Ke karamar hukumar Sokoto ta arewa, jaridar Leadership ta rahoto.

Umar ya tarbi sabbin ‘ya’yan PDPn ne a wani taron kaddamar da kungiyar ci gaban tsohuwar kasuwar Ubandoma/Sagir Mainiyo da kuma kaddamar da shirin bayar da tallafi da kungiyar ta kafa a yankin karkashin shugabancin shahararren dan kasuwa, Alh Abdulrashid Maccido.

Kara karanta wannan

Yadda Gwmanan Jihar Ebonyi Ya Nuna Gyan Bayan Karara Ga Dan Takarar Jami'iyyar APC

APC da PDP
2023: Dubban ‘Ya’yan Jam’iyyar APC Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Sokoto Hoto: PM News
Asali: UGC

Umar wanda shine kuma Mallam Ubandoma Sokoto, ya ba masu sauya shekar tabbacin cewa zai tafi da kowa a harkokin jam’iyyar musamman a yanzu da aka fara yakin neman zabe. Kuma da izinin Allah PDP ce za ta lashe zabe mai zuwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bukace su da su kara himma wajen samo Karin magoya baya da tallata jam’iyyar da yan takararta a yankin.

Dan takarar gwamnan ya roki al'ummar Sokoto da su sake zabar PDP don ci gaba da kwankwadar romon damokradiyya

Har ila yau, Umar ya jaddada cewa ta hanyar tara mutane daga matakin kasa ne PDP zata iya tsige APC da kuma shugabancin Najeriya mai ci a yanzu.

A jihar Sokoto, Umar ya ce gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal tana iya bakin kokari wajen tabbatar da masu zabe sun kurbi romon damokradiyya.

Kara karanta wannan

Atiku Na Kara Samun Karfi Yayin da Mambobin APC 1,000 Suka Sauya Sheka Zuwa PDP a Wata Jahar Kudu

Ya yi amfani da damar wajen rokon al’ummar jihar da su sauke ba jam’iyyar wata dama don ci gaban shugabanci nagari a zabe mai zuwa.

Ana ganin yankin Maniyo a matsayin daya daga cikin wuraren da jam’iyyar APC ke da karfi a jihar.

Gwamnatina zata tallafawa mata da matasa

Da yake bayyana manufarsa game da shirin tallafin, dan takarar gwamnan ya ce idan aka zabe shi, gwamnatinsa zata samar da damammaki ga matasa da mata a jihar Sokoto.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta bayar da fifiko wajen tallafawa matasa da mata a bangarori daban-daban.

Ya jinjinawa shugaban kungiyar, Alh Abdulrashid Maccido, kan tallafawa maza da mata a yankin sannan ya bukaci sauran yan kasuwa a jam’iyyar da su yi koyi da shi.

Kimanin mutum 300 ne suka amfana daga shirin inda aka rarraba masu babura, kekunan dinki, buhuhunan shinkafa da bandir-bandir na atampopi.

Ya samu rakiyar kwamishinoni a ma’aikatun harkokin kananan hukumomi, lafiyar dabbobi da kifaye, kasuwanci, Hon Abdullahi Maigwandu, Professor Abdulqadir Junaidu, da Hon. Bashir Gidado, rahoton Thisday ta rahoton.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Gamu da Cikas, Hadiman Gwamnan Arewa Sun Fice Daga PDP Zuwa Wata Jam'iyya

Sauran sune shugabannin kananan hukumomin Sokoto ta arewa da Sokoto ta kudu, Mustapha Shehu Sokoto, da Faruku Sayudi.

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta rasa wasu mambobinta a jihar Lagas inda suka fice zuwa PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel