Bidiyon Wankan Kwalisan Wani Matashi da Atamfa Ya Matukar Kayatar da Jama’a

Bidiyon Wankan Kwalisan Wani Matashi da Atamfa Ya Matukar Kayatar da Jama’a

  • Bidiyon TikTok na wani matashi ya yadu a soshiyal midiya bayan ya bayyana irin tsarin gayun shi da salon kwalisar shi
  • A bidiyon da yanzu yake yawo, an gan shi sanye cikin atamfa riga da wando wacce aka yi fentin motarsa har da jakarsa duk da irinsu
  • Mutane da yawa sun sha mamaki amma kuma ya matukar birge wasu wadanda suka dinga mamakin daga wacce jiha yake

Idan aka ce harkar gayu da kwalisa ake magana, wasu mutane sai dai a shafa fatiha domin sai sun yi yadda suka birge kowa da salon da ba a taba gani ba.

Wankan Kwalisa
Bidiyon Wankan Kwalisan Wani Matashi da Atamfa Ya Matukar Kayatar da Jama’a. Hoto daga TikTok/atomikkhamissou
Asali: UGC

Wani matashi ya bar mutane masu yawa baki bude inda suke ta martani bayan bidiyonsa na TikTok ya yadu wanda ya nuna tsarin iya shigarsa wanda ba kowa ke da irin shi ba.

Kara karanta wannan

Budurwa ta Zabgawa Saurayi Guba a Lemo, Manajan Otal ya Gaggauta Tona mata Asiri

A bidiyon, an ga mutumin sanye da atamfa mai launin bula da kuma kimono da ya saka a saman rigarsa tare da damammen wando.

A tsintsiyar hannunsa kuwa, wani irin agogo ne na kwalisa da gayu wanda shi kadai ya san wannan salon.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga bidiyon dai ku kalla da idanun ku:

Soshiyal midiya tayi martani

Bidiyon wanda tuni ya yadu, ya bar ma’abota amfani da yanar gizo baki bude inda wasu ke ta tofa albarkacin bakinsu kan wannan hazakarsa da salon gayu.

Duba wasu daga cikin tsokacin da Legit.ng ta tattaro:

just_kathyd:

“Wannan garkuwar imani ne?”

lamourameer222:

“Kai… A gaskiya wannan ya matukar birge ni. Wasu dai suna da matukar hakuri da kuma hazaka mai yawa.”

ucciseven:

“Ya kamata a ce an adana wannan salon kirkirar a wani wuri.”

Leolaa:

Kara karanta wannan

Bidiyo: An Gano Wata Babbar Mota Cike Da Kudi Yan N1000 Daga Arewa

“Agogon hannun ne ni yafi birge ni.”

Kayynova:

“A gaskiya agogon hannun ya tsone min idanu.”

we_sew_africa:

“Ban fusata ba gaskiya, ina kaunar gayun.”

Oktoquark:

“Motar tayi kyau tare da kwalisa.”

Muskaana:

“Gucci kanta ba za ta iya ba.”

Kriisti_kristal:

“Abun ya bani dariya amma kuma akwai hazaka.”

Jama’a da yawa kan dauka salon gayun da sai an dinga magana a kai, wasu ya birge, wasu kuwa akasin hakan.

Sau da yawa an fi samun irin salon gayun dake janyo cece-kuce daga mata wadanda basu yarda sun zubar da makaman wankansu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel