Dalilin Da Yasa Ya Zama Wajibi Shugaba Buhari Ya Yi Sulhu da 'Yan IPOB Gabanin Zaben 2023, Primate Ayodele

Dalilin Da Yasa Ya Zama Wajibi Shugaba Buhari Ya Yi Sulhu da 'Yan IPOB Gabanin Zaben 2023, Primate Ayodele

  • Primate Elijah Ayodele ya aikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da muhimmin sako gabannin babban zaben 2023
  • Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual ya bukaci shugaban kasar Najeriya da yayi sulhu da Nnamdi Kanu da Sunday Igboho don magance matsalar kasar kafin zaben 2023
  • Malamin addinin ya ce yakamata shugaban kasar yayi zaman sulhu don gujema rikicin da aka shirya don kawo cikas ga zabe mai zuwa

Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sasanta da kungiyoyin aware na Biyafara da kasar Yarbawa don samun zaman lafiya a zaben 2023.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinsa, , Osho Oluwatosin, Primate Ayodele ya ce masu fafutukar na shirin haddasa rikici a lokacin zaben, kuma yanzu ne ya dace a guje ma duk rikicin da ake shirin tayarwa a zaben 2023, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

2023: Kada Yan Najeriya Su Cire Rai, APC Zata Kawo Canjin da Suke Bukata, Tinubu

Buhari da Ayodele
Dalilin Da Yasa Ya Zama Wajibi Shugaba Buhari Ya Yi Sulhu da 'Yan IPOB Gabanin Zaben 2023, Primate Ayodele Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Dalilin da yasa akwai bukatar Buhari ya dauki matakin gaggawa, malamin addini

Malamin addinin ya bukaci gwamnati da kada ta raina yan awaren don gudun yin kuskure da zai hargitsa zaman lafiyar kasar, rahoton PM News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bukaci cewa gwamnatin ta kira su don yin sulhu da daidaita abubuwa cikin lumana.

Primate Ayodele ya gargadi Buhari da yayi taka-tsan-tsan a lamarin Nnamdi Kanu.

Ya ce:

“Iya dadewar Nnamdi Kanu a gidan yari, iya yadda za a dunga samun tashin hankali a kudu maso gabas. Idan suna son zaman lafiya a yankin, yan siyasar da ke da hannu a lamarin su janye. Yakamata gwamnati ta daina garkame shi. Idan yana da laifi, a bari a hukunta shi, idan bai da shi, a sake shi, wannan shine tsarin zaman lafiya.”

Kada a bari jam'iyyun siyasa su tsoma baki a harkokin INEC, Primate Ayodele ga Shugaban hukumar zabe

Kara karanta wannan

2023: Babban Malami a Najeriya Ya Aike da Sakon Gargadi Ga Shugaban INEC Na Kasa

Legit.ng ta kawo a baya cewa Primate Ayodele ya gargadi shugaban hukumar INEC a kan kada ya baiwa jam'iyyun siyasa damar yin katsalandar a harkokin hukumar gabannin zaben 2023.

Malamin addinin ya shawarci Yakubu Mahmood da ya zamo mai kishin kasa ko don ci gaba da wanzuwar Najeriya a matsayin daya bayan babban zabe mai zuwa.

Ya kuma ja hankali kan tabbatar da an yi amfani da na'urar BVAS wajen aika sakamakon zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel