Kano: Hisbah Ta Kama Mabarata 931, Ta Ce Wasunsu Yan Leken Asirin Yan Fashi Ne Da Sauran Bata Gari

Kano: Hisbah Ta Kama Mabarata 931, Ta Ce Wasunsu Yan Leken Asirin Yan Fashi Ne Da Sauran Bata Gari

  • Hukumar Hisbah ta Kano ta ce jami'anta sun yi nasarar kama mabarata a kalla guda 931 a tituna jihar a yunkurinta na hana bara
  • Babban kwamandan Hisbah, Muhammad Harun Ibn Sina ne ya bayyana hakan yayin da ya ke yi wa manema bayani kan ayyukan hukumar
  • Ibn Sina ya ce wasu daga cikin mabaratan yan leken asiri ne na yan fashi da makami da barayin waya da wasu bata gari

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce ta fara kama masu bara a titunan jihar, har ta yi nasarar kama mabarata 931 cikin makonni biyu, Daily Trust ta rahoto.

Hisbah ta koka cewa bata gari na amfani da wasu mabaratan a matsayin yan leken asiri, hakan na barazana ga zaman lafiyar jihar.

Yan Hisbah
Kano: Yan Fashi Da Masu Leken Asiri Suna Basaja Sa Sunan Bara, In Ji Hisbah. Hoto: @daily_trust.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babban kwamandan Hisbah, Muhammad Harun Ibn Sina, ne ya sanar da hakan a Kano yayin yi wa manema labarai kan ayyukan hukumar.

Ya ce wasu daga cikin wadanda ake zargin suna amfani da bara don aikata wasu muggan ayyuka.

Kalamansa:

"A kokarin mu na hana bara a titunan Kano, Hisabah ta Kano ta kama mabarata kimanin guda 931 a cikin makonni biyu, wasu daga cikinsu matasa ne masu karfi a jiki, mata da yara da ke yawo a titunan Kano daga safe har dare.
"Babban abin da ke damun mu shine wasunsu na amfani da bara don aikata munanan abubuwa kamar karuwanci da satar waya. Sun barci a kangon gini, shagunan kasuwanni da karkashin gada. Wasu mata daga cikinsu ma na da juna biyu, wasunsu kuma motocci sun buge shi yayin bara."

Ya cigaba da cewa:

"Mun mayar da wadanda ba yan Kano ba jihohinsu, yayin da yan Kano kuma mun sada su da iyalansu.
"Cikin wadanda muka kama, 611 mata ne, 211 maza ne. Mun sada mata 573 da maza 278, daga cikinsu 53 yan wasu jihohi ne."

Ya kuma ce duk mabaratan da aka kama karo na biyu za a hukunta su.

Kwamandan na Hisbah ya kuma ce yara mabarata da ba a gano yan uwansu ba, za a tura su makarantun sauya tunani da gyaran hali.

Jami'an Hisbah sun damke mabarata 648 a titunan Kano

A wani rahoton, Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta damke mabarata 648 a birnin Kano sakamakon zarginsu da take da karya dokokin haramta bara a titunan jihar tun daga watan Fabrairu.

Kakakin rundunar hukumar Hisbah, Lawan Ibrahim, ya ce wadanda ake zargin an kama su ne a yankunan Bata da ke kan babban titin Murtala Muhammed, asibitin Nasarawa, filin jirgin kasa da kuma wurin Yahuza Suya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel