Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan Ya Yi Babban Rashi

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan Ya Yi Babban Rashi

  • Allah ya yi wa Muhammad Isa, mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban majalisar dattawa rasuwa
  • Isa ya rasu ne a ranar Juma'a yayin da ake masa magani bayan hatsarin mota da ta ritsa da shi a hanyar Minna zuwa Suleja
  • Ahmad Lawan, shugaban majalisar Najeriya ya mika ta'aziyya ga iyalan mammacin da gwamnati da mutanen Katsina, ya yi addu'ar Allah ya gafarta masa

Mohammed Isa, daya daga cikin hadiman shugaban majalisar dattawar Najeriya, Lawan Ahmad a bangaren watsa labarai ya rasu.

Kamar yadda The Nation ta rahoto, Isa ya rasu ne yayin da ake masa magani bisa rauni da ya samu a hatsarin mota, a cewar Ola Awoniyi mataimaki na musamman (watsa labarai) na shugaban majalisa.

Mohammed Isa
Hadimin Shugaban Majalisar Dattawar Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ya Birne Ɗansa, Manyan Ƴan Siyasa Sun Halarci Jana'izar Don Yin Bankwana

Wani sashi na sanarwar ya ce:

"Tare da cikakken mika wuya ga Allah, muna bakin cikin sanar da rasuwar Mohammed Abdulkadir Isa, mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban majalisar dattawa.
"Isa ya rasu a ranar Juma'a da dare yayin da ake masa magani saboda rauni da ya yi sakamakon hatsarin mota a ranar Lahadi a hanyar Minna zuwa Suleja, jihar Niger.
"Za a yi jana'izarsa a yau da rana a Funtua, jihar Katsina bisa koyarwar addinin musulunci.
"Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya nuna bakin cikinsa bisa rasuwar Isa."

Lawan ya yi jimamin rashin Isa

Lawan ya bayyana rasuwar Isa a matsayin abu mai ban tsoro, mai ratsa zuciya da babban rashi.

Ya ce Isa mutum ne wanda ke da himma wurin aikinsa, ba a taba samunsa da gazawa ba kuma kwararre ne a aikinsa na jarida, Daily Trust ta rahoto.

Lawan ya mika sakon ta'aziyya

Kara karanta wannan

Sauye-Sauyen NNPC: "Rayuwa Ta Na Cikin Hatsari", Kyari Ya Yi Magana Kan Barazanar Kashe Shi

Lawan ya yi ta'aziyya ga iyalansa, abokin aikinsa da kungiyar jarida ta Najeriya (NUJ) bisa wannan rashin.

Shugaban majalisar ya kuma yi wa gwamnati da mutanen jihar Katsina ta'aziya kan rasuwar Isa.

Lawan ya yi addu'ar Allah ya bawa masoyansa juriya da hakurin rashinsa, ya yafe masa kura-kurensa ya saka masa da aljanna firdausi.

Allah Ya Yiwa Hadimin Gwamnan Nasarawa Rasuwa

A wani rahoto, Allah ya yi wa mai ba wa gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa shawara kan ayyuka na musamman, Alhaji Murtala Lamus, rasuwa a ranar Talata, 25 ga watan Oktoba.

Babban sakataren labaran Gwamna Sule, Ibrahim Addra ne ya tabbatar da rasuwan Lamus a cikin wata sanarwa da ya fitar, Sahara Reporters ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel