Tsohon Sarkin Kano, Sanusi II, Ya Samu Karuwar Diya Mace Tare Da Amaryarsa

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi II, Ya Samu Karuwar Diya Mace Tare Da Amaryarsa

  • Gimbiya Sa'adatu Barkindo, amaryar tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ta santalo kyakkyawar diya mace
  • Sabuwar jinjirar wacce aka sanyawa suna Zainab Khautar ita ce diya ta biyu a tsakanin ma'auratan
  • Sa'adatu dai ita ce autar matan khalifan na darikar Tijjaniya kuma diya ce a wajen Barkindo Aliyu Musdafa, Lamidon Adamawa

Allah ya azurta tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, da samun karuwar diya mace tare da amaryarsa, Sa’adatu Barkindo.

Kamar yadda shafin Linda Ikeji ya rahoto, an radawa kyakkyawar jinjirar suna da Zainab Khausar.

Sanusi II da Sa'adatu da jinjirarsu
Tsohon Sarkin Kano, Sanusi II, Ya Samu Karuwar Diya Mace Tare Da Amaryarsa Hoto: LIB
Asali: UGC

Khausar ita ce diya ta biyu da ke tsakanin tsohon basaraken da amaryar tasa wacce ita ce ta hudu a cikin matansa.

Tsohon sarkin ya auri Sa’adatu wacce diya ce ga Lamidon Adamawa, Barkindo Aliyu Musdafa, a shekarar 2015.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wasu Fitattun Malamai Biyu a Jihar Arewa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sun haifi diyarsu ta farko mai suna Halimatu Sadiya a ranar 5 ga watan Mayun 2020.

A cikin wasu hotuna da suka yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano mai jego tare da uwayen gidanta dauke da sabuwar jinjira yayin da suka kasance cike da farin ciki. A wani hoton kuma, an gano ta tare da diyar sarkin, Saheeda.

Alamu sun nuna akwai dankon soyayya, fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin wannan iyali domin a koda yaushe a kan gano su tare cikin girmamawa.

Jama'a sun taya su murna

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:

prof_tabitha ta yi martani:

“Ina taya ku san barka.”

utchly_fragrances ta rubuta:

Oh wow! Ina taya ku san barka yallabai da yallabiya. Barka da zuwa ya ke kyakkyawar jinjira .”

iam_bmodel ya ce:

Kara karanta wannan

Rikicin Makiyaya da Manoma Ya Barke, An Yi wa Kauyuka 10 Kaca-kaca a Jihar Kano

“Ina masa san barka. Daya daga cikin yan arewa da nake garin mutuncinsa sosai .”

segun.adegoke ya ce:

“Lamido Sanusi Lamido, dan arewa mafi daraja da ke burgeni. Ina maka san barka.”

fannah_essentials ta rubuta:

Masha Allah, Allah Ya raya bisa tafarki na addinin islam ameen....ina masu son barka su duka biyun.”

alaga_iworoad ya rubuta:

"Kausara."

mirabel_davemario

"Toh, ina masu son barka."

chazedegrimm ya ce:

"Ana yiwa sabuwar jinjira barka da zuwa, kyakkyawar sarauniya."

billy_rashfabrics:

"Ina yi masu san barka. Tambayata shine, shin ita din gimbiya ce? ko?"

Asali: Legit.ng

Online view pixel