Shugaba Buhari Ya Kaiwa Sabon Sarkin Birtaniya Ziyara Yau Laraba

Shugaba Buhari Ya Kaiwa Sabon Sarkin Birtaniya Ziyara Yau Laraba

  • Karon farko, Shugaba Muhammadu Buhari ya hadu da Sabon Sarkin Ingila, HRM Charles Na Uku
  • Shugaba Buhari bai samu daman halartan taron nadin sarautan Sarkin Charles ba da jana'izar mahaifiyarsa
  • Shugaba Buhari ya yi takakkiya zuwa fadar Sarki CHarles domin tayashi murna

Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara ta musamman fadar Sarkin Ingila, Sarki Charles III a fadar Buckingham Palace dake birnin Landan.

Shugabannin biyu sun hadu ne ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamba, 2022.

Hadimin Buhari kan kafafen yada labaran zamani, Bashir Ahmed ya bayyana hakan inda ya saki hotunan ziyarar.

Buhari
Shugaba Buhari Ya Kaiwa Sabon Sarkin Birtaniya Ziyara Yau Laraba Hoto: BashirAhmaad
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tafiyar Buhari Landan

Jirgin Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Landan, kasar Birtaniya lafiya cikin daren Talata, 1 ga watan Nuwamba, 2022.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotu Ta Bada Umurnin A Jefa Shugaban EFCC, Rashid Bawa, Gidan Yari

Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmed, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar.

Yace:

"Shugaba Muhammadu Buhari ya dira Landan, UK domin ganin Likita kamar yadda ya saba. Shugaba kasan zai dawo kasar a mako na biyu cikin Nuwamba, 2022."

Abin Da Yasa Buhari Ke Tsallake Likitocin Nigeria Ya Tafi Landan Duba Lafiyarsa, Adesina

Mashawarci na musamman ga Shugaban Kasa kan kafafen watsa labarai, Femi Adesina, ya ce mai gidansa ya fi son zuwa Birtaniya a duba lafiyarsa ne don likitocin Nigeria ba su da bayansa na lafiya, The Punch ta ruwaito.

Adesina ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambaya kan dalilin da yasa Buhari ba ya yarda likitoci su duba shi a Nigeria yayin wani shiri a gidan talabin na Channels Television.

A cewarsa, likitocin Burtaniya ne kadai suka da bayanan lafiyar Buhari.

Ya kara da cewa tun kimanin shekaru 40 da suka gabata likitocin na Burtaniya ne da duba lafiyar shugaban kasan.

Kara karanta wannan

Gwamna Lalong Ya Shigar Da Ali Nuhu, Duniyar Kannywood Yakin Neman Zaben Tinubu/Shettima

Ya ce:

"Shugaban kasar ya dade tare da likitoci da tawagar masu kulawa da lafiyarsa fiye da shekaru 40.
"Abin da ya fi dacewa shine ya cigaba da wadanda suka san bayannan lafiyarsa shi yasa ya ke zuwa Landan don ganinsu. Su ke duba shi fiye da shekaru 40 da suka shude. Idan za ka iya biya, toh ka cigaba da zuwa wurin wadanda ke da bayyanan lafiyarka."

Asali: Legit.ng

Online view pixel