Shugaba Muhammadu Buhari Ya Dira Landan Don Ganin Likita

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Dira Landan Don Ganin Likita

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya isabirnin Landan inda bayan barin babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, a ranar Litinin
  • Kamar yadda mai bashi shawara na musamman kan yada labarai da hulda da jama’a, Femi Adesina ya bayyana, zai je duba lafiyarsa ne
  • Adesina ya sanar da cewa ana tsammanin Buhari ya dawo Najeriya a mako na biyu na watan Nuwamba bayan kammala duba lafiyarsa

Jirgin Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Landan, kasar Birtaniya lafiya cikin daren Talata, 1 ga watan Nuwamba, 2022.

Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmed, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar.

Yace:

"Shugaba Muhammadu Buhari ya dira Landan, UK domin ganin Likita kamar yadda ya saba. Shugaba kasan zai dawo kasar a mako na biyu cikin Nuwamba, 2022."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ifeanyi Adeleke, Yaron Shahrarren Mawaki, Davido, Ya Mutu Cikin Swimming Pool

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abin Da Yasa Buhari Ke Tsallake Likitocin Nigeria Ya Tafi Landan Duba Lafiyarsa, Adesina

Mashawarci na musamman ga Shugaban Kasa kan kafafen watsa labarai, Femi Adesina, ya ce mai gidansa ya fi son zuwa Birtaniya a duba lafiyarsa ne don likitocin Nigeria ba su da bayansa na lafiya, The Punch ta ruwaito.

Adesina ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambaya kan dalilin da yasa Buhari ba ya yarda likitoci su duba shi a Nigeria yayin wani shiri a gidan talabin na Channels Television.

A cewarsa, likitocin Burtaniya ne kadai suka da bayanan lafiyar Buhari.

Ya kara da cewa tun kimanin shekaru 40 da suka gabata likitocin na Burtaniya ne da duba lafiyar shugaban kasan.

Ya ce:

"Shugaban kasar ya dade tare da likitoci da tawagar masu kulawa da lafiyarsa fiye da shekaru 40.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari Zai Bar Najeriya Zuwa Landan, An Bayyana Abinda Zai je Yi

"Abin da ya fi dacewa shine ya cigaba da wadanda suka san bayannan lafiyarsa shi yasa ya ke zuwa Landan don ganinsu. Su ke duba shi fiye da shekaru 40 da suka shude. Idan za ka iya biya, toh ka cigaba da zuwa wurin wadanda ke da bayyanan lafiyarka."

Buhari ya fi galibin matasar da ke sukansa lafiya, Garba Shehu

Garba Shehu, kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce shugaba Buhari ya fi matasa da dama da ke caccakar sa lafiya da kwarin jiki.

Wasu hotunan shugaba Buhari ya tsuke da kananun kaya a Belgium, wanda bai saba sanyawa ba sun fara yaduwa a kafafen sada zumunta wanda suka janyo cece-kuce iri-iri.

Yayin da aka bukaci tsokacin Shehu akan shigar cewa ya yi ‘yan Najeriya sun fara yarda da cewa shugaban kasa yana cikin koshin lafiya bayan ganin hotunan nashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel