Kotu Ta Umurci Sifeto Janar Na Yan Sanda Ya Tasa Keyar Shugaban EFCC Zuwa Kurkuku

Kotu Ta Umurci Sifeto Janar Na Yan Sanda Ya Tasa Keyar Shugaban EFCC Zuwa Kurkuku

Babba kotu dake zamanta a unguwar Maitama birnin tarayya Abuja ta kama Shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) da laifi.

Alkalin kotun, Chizob Orji, ya kama Abdulrasheed Bawa da laifin saba umurnin da kotun tayi tun shekarun baya.

Saboda haka ya umurci hukumar yan sanda ta damke Abdulrasheed Bawa da gaggawa kuma a jefashi kurkukun Kuje har sai ya bi umurninsa.

Bawaa
Kotu Ta Umurci Sifeto Janar Na Yan Sanda Ya Tasa Keyar Shugaban EFCC Zuwa Kurkuku Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkali Chizoba yace:

"Shugaban EFCC ya ki bin umurnin da wannan kotu tayi ranar 21 ga Nuwamba 2018 inda ta umurnin hukumar ta mayarwa wanda ya shigar da kara motarsa Range Rover (Super charge) da N40, 000,000.00 (Forty Million Naira)."
"Saboda saba wannan umurni na kotu, a jefashi kurkukun Kuje bisa raina hankalin kotu da saba umurnin da tayi ranar 21 ga Nuwamba 2018, har sai lokacin da ya bi umurnin."

Kara karanta wannan

Bacin rana: Kotu ta daure mai gadi a jihar Arewa bisa laifin barci a bakin aiki

"Sifeto Janar na yan sanda ya tabbatar da cewa an bi wannan umurni."

Alkalin ya yi watsi da uzurin da Lauyan EFCC, Francis Jirbo, ke kokarin badawa kan rashin bin umurnin.

TheNation tace yau Talata ta ga takardar umurnin da aka yi ranar 28 ga Oktoba mai lamba FCT/HC/M/52/2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel