Yan Sanda Sun Kama Wasu Matasa Bisa Zargin Tube Wata Mata da Dukanta a Enugu

Yan Sanda Sun Kama Wasu Matasa Bisa Zargin Tube Wata Mata da Dukanta a Enugu

  • 'Yan sanda sun kama wasu mutane Shida da ake zargi da hannu a lakaɗa wa wata mata dukan tsiya a jihar Enugu
  • Bayanai sun nuna cewa matasan na zarginta da gurbata musu wurin ibada, suka tuɓe ta tsirara suka haɗa da wani ɗan uwanta
  • Kakakin yan sandan Enugu, Daniel Ndukwe, yace suna ci gaba da bincike da nufin cafke sauran mutanen

Enugu - Hukumar 'yan sanda reshen jihar Enugu tace ta damƙe wasu mutum Shida da take zargi da tuɓe wata mata tsirara kana suka ci zarafinta a jihar.

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a, kamar yadda Jaridar Premium Times ta ruwaito.

Yan sanda sun kama mutum 6.
Yan Sanda Sun Kama Wasu Matasa Bisa Zargin Tube Wata Mata da Dukanta a Enugu Hoto: premiumtimes
Asali: Twitter

Lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Oktoba, 2022 a yankin Agunese, Afam-Mmaku, wani kauye a ƙaramar hukumar Awgu, jihar Enugu.

Kara karanta wannan

Wani Magidanci Ya Halaka Ɗiyar Cikinsa Kan Ta Kama Masa Mazantaka

Matasan ƙauyem sun zargi matar mai suna, Anthonia Okonkwo, da gurbata musu wuri mai tsarki ta hanyar noman dodon koɗi a kusa da wurin. Zargin da matar ta musanta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Misis Okonkwo, tace kowa ya santa tana sana'ar noma dodunan koɗi a ƙauyen kuma ta siyarwa mutane tsawon lokaci domin ta kula da yaranta huɗu tun bayan mutuwar majinta shekaru 13 da suka shuɗe.

Yadda lamarin ya faru

Da take labarta yadda lamarin ya auku, Okonkwo tace wata rana tana zaune a cikin gida sai kawai ta jiyo cece-kuce a waje, ba zato wasu matasa suka kutsa kai suka jawota waje ba tare da sauraronta ba.

A cewarta, nan take matasan suka fara lakaɗa mata duka da makamai da Bulalu, suka tuɓe mata kaya, suka ɗaura mata ganyen dabino a ƙugu da wuya, alamar dake nuna ta aikata saɓo a yankin.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Bude Wa Mutane Wuta Ana Tsaka da Cin Kasuwa, Sun Tafka Barna a Jihar Arewa

Wane mataki aka ɗauka?

Kakakin yan sandan yace tuni jami'an tsaro sun yi ram da mutum shida daga cikin matasan da suka jagoranci aikata wannan ɗanyen aiki, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Ya kuma ambaci sunayensu da Maduabuchi Madueke, Obioma Nwangene, da Stan Okoro, da ake zargi ta jan ragamar sauran, sai kuma Samuel Anikene, Chukwuebuka Agu, da Jonathan Nwangene, da suke biye musu.

"Ana cigaba da bincike da nufin lalubo sauran masu hannu a lamarin, " Inji DSP Ndukwe.

Yace a binciken da dakaru suka gudanar, waɗanda ake zargin sun haɗa da ɗan uwan matar suka lakaɗa masa duka yayin da ya yi yunkurin taimaka mata, sun ji masa raunuka.

A wani labarin kuma Miji Ya Fadi Yadda Ya Kama Matarsa Dumu-Dumu Tana Saduwa da Dan Uwansa, Ya Nemi Saki a Kotu

Wani Magidanci ɗan kasuwa, Justine Onu, ya nemi wata Kotu a Abuja ta raba aurensa da Joyce bisa zargin ganinta ta kwanta da ɗan uwansa.

Kara karanta wannan

'Na Gaji da Wannan Auren A Raba Mu' Wata Mata Ta Fada Wa Kotun Musulunci Cin Kashin da Mijinta Ke Mata

Mutumin ya faɗa wa Alkali cewa matar bata kula da shi, yayansa da sauran iyalai, burinta kawai ta kwanta kowa ta samu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel